Nyesom Wike Ya Bada Umarnin Ruguza Shaguna Yayin da Ake Cigaba da Rusau a Abuja
- Hukumar FCTA ta rusa shagunan kwano da mutane su ka kafa a wasu wurare da ke birnin Abuja
- Mukhtar Galadima ya shaida cewa Ministan tarayyar Abuja, Nyesom Wike, ya bada umarnin hakan
- Wike bai son ganin shaguna a yankunan da gwamnati ta tsara domin yin wasu abubuwan dabam
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Abuja - Hukumar FCTA mai kula da gudanar da birnin tarayya Abuja ta rusa wasu shaguna a yankin Kabusa a garin Abuja.
Rahoton NAN ya tabbatar da cewa an rugurguza wasu shaguna a mazabar Dutse da ke Abuja, inda mutane su ke neman na abinci.
Darektan kula da cigaban gine-gine a FCTA, Mukhtar Galadima wanda ya jagoranci wannan aiki, ya bayyana makasudin hakan.
Menene dalilin rusa shaguna a Kabusa?
Malam Mukhtar Galadima ya sanar da manema labarai an cire gine-ginen da aka yi ba tare da ka’ida ba ne domin a tsabtace wurin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar Galadima, shagunan da aka yi sun kawo cunkoso a shatale-talen, wanda hakan ya bata tsarin da hukuma tayi wa Abuja.
FCTA: "Umarnin Nyesom Wike ne"
Jami’in hukumar ya tabbatar da cewa wannan ya na cikin umarnin da aka samu daga ministan birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike.
Bayan zamansa minista a Agustan nan, Nyesom Wike ya ba FCTA umarni cewa ka da a bar wani shagon rumfa a babban birnin kasar.
Hukumar ta ke cewa tun asali inda aka cika da shagunan saye da sayarwar wuri ne da ya kamata gwamnatin tarayya ta gina gada.
"Ruguza shagunan ya na cikin cigaban yunkurin tsabtace birnin Abuja domin a samu lafiyar muhalli.
Kabusa ya zama maruru mai wuyar matsewa ga mutanen da su ke shigo domin shaguna sun cika ko ina.
An tanadi wurin ne domin zirga-zirga, da niyyar za ayi gadar sama da za ta hada titunan biyu da babbar hanya."
- Mukhtar Galadima
"Za mu fara daga nan zuwa shatale-talen Galadima. Idan mu ka kora wadanda su ka cika wurin, za mu zo da tsari mai kyau da zai dauki duka ‘yan kasuwa."
- Mukhtar Galadima
Aikin jirgin kasan Abuja
Rahoton da mu ka samu shi ne Shugaban Najeriya ya nuna bai bukatar a raba masa filaye a Abuja, illa ministansa ya kawo cigaba.
Bola Ahmed Tinubu ya bukaci Nyesom Wike ya gaggauta kammala aikin titin jirgin kasan birnin Abuja, shi kuma ya dauki aniya.
Asali: Legit.ng