Tinubu Ya Waiwayi Ma’aikata, Ya Koka Kan Yawan Wadanda Ke Cinye Albashin Gwamnati
- Bola Ahmed Tinubu ya karbi bakuncin shugabannin kamfanin fasahar nan na Oracle a ofishinsa
- Shugaban Najeriyan zai zo ayi amfani da fasahohin zamani wajen gyara sha’anin aikin gwamnati
- Tinubu ya fara kuka da adadin ma’aikatan gwamnatin da su ke cinye albashi a tarayya da jihohi
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Abuja - Bola Ahmed Tinubu ya nuna damuwarsa game da tulin ma’aikatan gwamnati da ake da su tun daga matakin jihohi zuwa tarayya.
Tribune ta ce Bola Ahmed Tinubu ya bayyana abin da yake cikin ran sa a lokacin da ya hadu da shugaban Oracle, Andres Garcia Arroyo.
Mista Garcia Arroyo wanda mataimakin shugaba ne a kamfanin fasaha na Oracle ya ziyarci Mai girma shugaban Najeriya a Aso Rock.
Ma'aikata su na tada hankalin Tinubu
Tinubu ya shaidawa masu ziyartarsa cewa idan aka yi amfani da fasaha, za a iya zamanantar da aikin gwamnati sannan a ci moriyar kudi.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Idan aka komawa fasahohi, shugaban kasar ya na ganin za a rika amfani da kudi yadda ya kamata, watanni uku bayan cire tallafin fetur.
The Cable ta rahoto labarin, ta ce shugaban na Najeriya ya shaida yadda yake firgita a duk lokacin da ya ga adadin ma’aikatan da ke ake da su.
Mai girma Tinubu ya na so kamfanin Oracle su taimakawa Najeriya wajen kawo dabarun da za su jawo gwamnatinsa ta rage fitar da kudi.
"A duk lokacin da su ka bani adadin ma’aikatan da ke karbar albashi, ina firgita sosai. Ina za mu samu kudin da ake bukata wajen gina abubuwan more rayuwa idan ma’aikatan da su ke 1% zuwa 2% na adadin al’umma su na cinye duka kudin shiga?
Ina tunanin mu na bukatar lura da matsi na fasaha ta yadda za mu duba duk wasu fitar kudi. Ina sa ran mu yi aiki da Oracle domin na yarda da ku cewa za ku iya domin kun yi hakan a baya."
- Bola Tinubu
Bola Tinubu ya yarda da Oracle
Gwamnatin Tinubu ta na maraba da gyara aikin gwamnati da tsarin tattara bayanai a Najeriya, ya ce ya yi aiki da Oracle sa'ilin ya na gwamna a Legas.
Har ila yau, gwamnatin tarayya ta nuna muhimmancin kirkiro makarantun horaswa a fadin kasar nan domin kara koyawa ma’aikatan gwamnati aiki.
Gaba da bayan Tinubu
Matsin lambar jama’a da ‘yan siyasa yana jawo Bola Tinubu ya canza shawara, an ji labari irin haka ya jawo aka cire Maryam Shetty daga Ministoci.
Tinubu ya hakura da rusa ma’aikatar Neja-Delta da ya fahimci za ayi masa ca, kuma saboda haka ne ya canza wasu daga cikin shugabannin NDDC.
Asali: Legit.ng