Sojojin Nijar Sun Sake Bude Sararin Samaniyar Kasar Ga Jiragen Jigila
- Sojojin juyin mulkin jamhuriyar Nijar, sun sanar da buɗe sararin samaniyar ƙasar ga jiragen jigilar fasinjoji
- Hakan na zuwa ne bayan shafe sama da wata ɗaya da sojojin suka yi a kan karagar mulki
- Sojojin sun rufe sararin samaniyar ne domin bai wa kansu kariya daga hare-haren da ECOWAS ka iya kawo mu su
Niamey, Nijar - Sojojin juyin mulkin jamhuriyar Nijar sun sanar da bude sararin samaniyar ƙasarsu ga jiragen jigilar fasinjoji bayan shafe sama da wata ɗaya a kan mulki.
Sojin na Nijar sun sanar da rufe sararin samaniyar ne jim kaɗan bayan kifar da gwamnatin hamɓararren shugaban ƙasar Mohamed Bazoum kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Dalilin rufe sararin samaniyar da sojojin Nijar suka yi
Sojojin Nijar dai sun rufe sararin samaniyar ne bayan juyin mulkin da suka yi wa Bazoum saboda bai wa kansu kariya daga hare-haren da suke tunanin za a iya kawo musu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƙungiyar raya tattalin arziƙin ƙasashen Afrika ta Yamma (ECOWAS), ta yi barazanar yin amfani da ƙarfin soji wajen dawo da mulkin dimokuradiyya a Nijar, inda har wa'adin kwanaki ta bai wa sojojin domin su mayarwa Bazoum kujerarsa.
Ƙungiyar ECOWAS, tarayyar Afrika (AU) da ma wasu kungiyoyi da ƙasashen duniya sun yi Allah wadai da juyin mulkin da sojin na Nijar suka yi gami da sanya mu su takunkumai kala-kala.
Kalubalen da rufe sararin samaniyar Nijar ya janyo
Rufe sararin samaniyar da sojin na Nijar suka yi ya sanya jiragen ƙasar Faransa da na ƙasashen Turai yin dogon zagaye idan za su je wata ƙasar ta Afrika kamar yadda Reuters ta ruwaito.
Nijar ta fi ƙasar Faransa faɗin ƙasa, wanda rufe sararin samaniyarta ya tilastawa wasu daga cikin kamfanonin jiragen saman Faransa haƙura da aiki a yankin.
Sojin Nijar sun bude sararin samaniyar a karon farko bayan kifar da gwamnatin Bazoum, sai dai sun sake rufewa a ranar 6 ga watan Agusta domin tsoron matakin da ECOWAS da sauran ƙasashe ka iya ɗauka a kansu.
Sai dai ranar Litinin, 4 ga watan Satumba ne sojin na jamhuriyar Nijar suka sanar da sake bude sararin samaniyar ƙasar.
Matukin jirgin sama ya mutu a yayin da ake sheƙa gudu
Legit.ng a baya ta yi rahoto kan wani matuƙin jirgi da ya rasa ransa a yayin da jirgin ke sheƙa gudu ɗauke da fasinja a sararin samaniya.
Direban jirgin ya faɗi ne a cikin banɗakin jirgin da ke ɗauke da fasinja 271, yayinda abokan aikinsa suka yi ƙoƙarin saukar da jirgin cikin gaggawa.
Asali: Legit.ng