Maryam Shetty, NDDC da Kwan Gaba-Kwan Baya 5 da Bola Tinubu ya yi a Wata 3

Maryam Shetty, NDDC da Kwan Gaba-Kwan Baya 5 da Bola Tinubu ya yi a Wata 3

  • Bola Ahmed Tinubu ya kusa shafe kwanaki 100 a kan karagar mulki a matsayin shugaban Najeriya
  • Shugabanni da sauran al’umma sun fito da wata al’ada ta auna rawar gwamnati bayan ta kwana 100
  • Tinubu ya nuna salon mulkinsa daga lokacin da ya karbi Muhammadu Buhari a Mayu zuwa yanzu

Abuja - Rahoton nan da irinsa ya fito daga Daily Trust ya duba kwan gaba-kwan baya da gwamnatin Bola Tinubu tayi daga watan Mayu zuwa yau.

Tinubu
Shugaba Bola Tinubu a Aso Rock Hoto: @Dolusegun
Asali: Twitter

1. Soke Ma’aikatar Neja Delta

Da farko an ga alamun Bola Tinubu zai soke ma’aikatar harkokin Neja-Delta, da surutun mutane ya yi yawa, sai ya dawo da ma’aikatar kuma ya nada mata minista.

2. Tinubu ya soma canza Ministoci

Kafin ya rantsar da ministocinsa, shugaban Najeriyan ya fara garambawul, ya canzawa Abubakar Momoh, Tunji Ojo, Saidu Alkali da Gboyega Oyetola wurin aiki.

Kara karanta wannan

Babu Mamaki Tinubu Ya Fatattaki Mutanen da Buhari Ya Ba Mukami Daf da Barin Mulki

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

3. Shetty zuwa Bunkure

An ji yadda Bola Tinubu ya bada sunan Maryam Shetty domin zama minista, amma a karshe ya cire sunanta, hakan ya yi sanadiyyar kawo Mariya Mahmud Bunkure.

4. Cire tallafin man fetur

Shugaban kasar ya cire tallafin fetur kuma ya hau kujerar na-ki, amma da ya fahimci za ayi masa zanga-zanga, dolensa ya fito ya yi wa ‘yan Najeriya dogon jawabi.

5. Sababbin shugabannin NDDC

Kwanaki aka nadawa hukumar NDDC shugabanni, amma da surutun jama’a ya yi yawa, sai aka ji gwamnatin tarayya ta janye nadin mukaman, ta canza wasu.

Maganar Muhammadu Sanusi II

An rahoto Muhammadu Sanusi II ya na cewa a an tafiyar da kasa babu masu ilmin tattalin arzikin kasa, kuma idan an fada gwamnatin tarayya ta ki sauraro.

Masanin tattalin arzikin ya ce sai da gwamnatin tarayya ta karbo aron N30tr a bankin CBN, a karshe kuwa bashi ya yi katutu, kudin shiga su ka kare a bashi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng