Gwamnatin Tarayya Zata Gana da Kungiyar Kwadago Kan Batun Yajin Aiki

Gwamnatin Tarayya Zata Gana da Kungiyar Kwadago Kan Batun Yajin Aiki

  • Gwamnatin tarayya ta fara yunkurin dakatar da ƙungiyoyin kwadago daga shiga yajin aikin gargaɗi na kwana 2
  • Ministan kwadago da samar da ayyuka, Simon Lalong ya roƙi NLC da kawayenta kada su tsunduma yajin aikin domin zasu maida hannun agogo baya
  • A cewarsa, ma'aikatar kwadago ta tarayya ta shirya zama kan wannan batu yau Litinin da misalin ƙarfe 3:00 na yamma

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT Abuja - Gwamnatin tarayya ta ce ta shirya ganawa da shugabannin kungiyoyin kwadago da misalin karfe 3 na yammacin yau Litinin domin dakile yunƙurinsu na shiga yajin aiki.

Jaridar Daily Trust ta ce Ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Simong Lalong, ne ya bayyana haka a wurin taron manema labarai da ke gudana yanzu haka a Abuja.

Ministan kwadugo da samar da ayyukan yi, Simon Lalong.
Gwamnatin Tarayya Zata Gana da Kungiyar Kwadago Kan Batun Yajin Aiki Hoto: Simon Lalong
Asali: UGC

Lalong ya yi bayanin cewa har zuwa yanzu bai gana da shugabannin ƙungiyoyin kwadago bane saboda bai samu cikakken bayanai daga ɓangarorin gwamnati da abin ya shafa ba.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Hukumar DSS Ta Bankado Shirin Tayar Da Tarzoma a Kasa, Ta Magantu Kan Masu Hannu a Ciki

FG ta aike da saƙo ga NLC da ƙawayenta

Ministan ya roƙi shugabannin ƙungiyar kwadago (NLC) da ƙungiyar 'yan kasuwa (TUC) da su dakatar da sauran ƙawayensu daga shirin tsunduma yajin aikin gargaɗi na kwana 2.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Haka zalika ya yi kira ga ƙungiyoyin baki ɗaya, su taimaka su janye kudirinsu na tsunduma yajin aikin sai baba ta gani a faɗin ƙasa wanda suka shirya mako uku bayan wannan.

Mista Lalong ya yi alkawarin cewa gwamnatin tarayya zata magance duk matsalolin da NLC ta koka a kansu idan aka ba ta lokaci ta gama kimtsawa a kan madafun iko.

Jaridar This Day ta rahoto Lalong na cewa:

"Ya zama wajibi mu yi kira ga shugabannin kungiyar kwadago ta Najeriya (NLC) su dakatar da yajin aikin gargadi na kwanaki biyu da suka yi niyyar shiga."

Kara karanta wannan

An sake shiga matsi: Ta'azzarar barnar 'yan bindiga ta sa an rufe kasuwannin shanu 8 a Arewa

"Domin irin wannan mataki zai yi illa ga nasarorin da gwamnati ta samu a ƙoƙarinta na samar da kyakkyawar makoma ga ma’aikatan Najeriya da ‘yan kasa baki daya."
“Bugu da kari kuma, ina bukatar shugabancin kungiyar kwadago ta Najeriya ta ba wa wannan gwamnati wani lokaci don ta shirya kuma ta warware matsalolin da ake fuskanta a kasar nan."

Jam'iyyar APC Zata Buɗe Ofisoshi a Gundumomi 8,813 a Najeriya

A wani rahoton kuma Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana sabon shirinsa na matso da jam'iyyar APC kusa da 'yan Najeriya.

Ganduje, shugaban jam'iyyar APC na ƙasa ya ayyana shirinsa na gina ofisoshin jam'iyyar a duka gundumomi sama da 8,000 da ke faɗin ƙasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262