Cire Tallafin Mai: Gwamnatin Neja Za Ta Farfado Da Biyan Dalibai Kudin Tallafin Karatu

Cire Tallafin Mai: Gwamnatin Neja Za Ta Farfado Da Biyan Dalibai Kudin Tallafin Karatu

  • Gwamna Mohammed Umaru Bago na jihar Neja ya sanar da tanadin da gwamnatinsa ke yi domin tallafawa al'ummarta musamman dalibai a wannan hali da ake ciki na matsin rayuwa
  • Gwamnatin jihar Neja tana shirin farfado da tsarin biyan dalibai yan asalin jihar da ke jami'a kudin tallafin karatu
  • Bago ya kuma ce suna shirin samar da manyan motoci masu amfani da gas don jigilar dalibai kyauta a makarantun jihar

Jihar Niger - A kokarin da take yi na ragewa al'umma radadin cire tallafin man fetur da gwamnatin tarayya ta yi, gwamnatin jihar Neja ta bayyana cewa tana shirin farfado da tsarin bai wa daliban jihar da ke karatu a jami’a kudin tallafi, Nigerian Tribune ta rahoto.

Gwamnan jihar, Mohammed Umaru Bago, ne ya sanar da shirin a wani taron manema labarai da ya gudana a gidan gwamnati da ke garin Minna, babban birnin jihar a ranar Juma’a, 1 ga watan Satumba.

Kara karanta wannan

Kwanaki 100 Kan Mulki: Tarun Matsaloli 3 Da Ke Hana Shugaba Tinubu Sakewa Tun Bayan Hawanshi Mulki

Gwamnatin Neja za ta fara ba dalibai tallafin karatu
Cire Tallafin Mai: Gwamnatin Neja Za Ta Farfado Da Biyan Dalibai Kudin Tallafin Karatu Hoto: Mohammed Umar Bago
Asali: Facebook

Gwamnati na sane da halin da al'umma ke ciki, Gwamna Bago

Ya yi bayanin cewa gwamnati na sane da wahalhalun da mutane ke sha, don haka akwai bukatar masu ruwa da tsaki a kowane mataki su marawa gwamnati baya domin ta samu damar shayar da al'umma romon damokradiyya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bago ya kuma bayyana cewa nan ba da dadewa ba, gwamnati za ta kaddamar da wasu motocin bas guda 200 da ke amfani da gas don jigilar dalibai kyauta a fadin jihar, rahoton Independent.

Ya kuma ce gwamnatin za ta kuma samar da wasu motocin guda 100 da zai dunga jigilar Suleja zuwa Abuja a kan farashi mai rahusa.

A wani lamari makamancin wannan, gwamnan ya ce manyan motocin bas 50 za su dunga jigilar mutane a Minna da kewaye sannan za a kaddamar da wasu 50 a fadin kananan hukumomi 25 na jihar.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa Dauki Yan Sa Kai 7,000 Aiki Don Magance Matsalar Rashin Tsaro

Ya kara da cewar:

"Ma'aikatan gwamnati ma za su amfana daga wannan bas din koda dai ragin kudin mota za a yi masu."

Legit.ng ta tattauna da wata yar jihar don jin ta bakinta dangane da wannan yunkuri da gwamnatin jihar ke yi.

Zainab Bako wacce tsohuwar daliba ce a jami’ar jihar ta ce:

“Wannan abu ne mai kyau amma idan an tsaftace tsarin, na tuna lokacin da nake makaranta zamanin tsohon Gwamna Babangida Aliyu muna ta samun N15,000 a matsayin tallafin karatu amma duk da haka abun baya ratsa kowa, kuma a wancan lokacin babu ma tsadar rayuwa kamar yanzu.
“Idan har gwamnatin Bago za ta jajirce don ganin wasu basu karkatar da akalar abun ba toh zai ragewa mutane zafi sosai.”

Gwamnan Neja ya bada hutun kwana 3 don rabon kayan tallafi

A wani labarin kuma, mun ji cewa gwamnatin jihar Neja ta ayyana hutun kwanaki uku daga Laraba, 6 ga watan Satumba zuwa Juma'a, 9 ga watan Satumba a fadin jihar.

A cewar Gwamna Mohammed Umar Bago, za a yi amfani da wannan damar ne wajen rabawa al'ummar jihar tallafin kayan abinci don rage masu radadin halin da ake ciki saboda cire tallafin mai da aka yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng