Rayukan Mutum biyu Sun Salwanta a Wani Hatsarin Mota a Jihar Ondo

Rayukan Mutum biyu Sun Salwanta a Wani Hatsarin Mota a Jihar Ondo

  • Rayukan mutum biyu sun salwanta a wani mummunan hatsarin mota da ya auki a jihar Ondo da ke yankin Kudu maso Yamma
  • Hukumar FRSC ta bayyana cewa wasu mutum biyar kuma sun samu raunika a hatsarin da ya auku a yankin Olokuta na jihar
  • Kwamandan hukumar na jihar ya yi kira ga masu ababen hawa da su riƙa bin dokokin tuƙi domin rage aukuwar haɗura

Jihar Ondo - Hukumar kiyaye haɗura ta ƙasa (FRSC) reshen jihar Ondo, ta tabbatar da aukuwar wani mummunan hatsarin mota akan titin Akure-Ondo.

Hukumar ta bayyana cewa mutum biyu sun halaka yayin da wasu mutum biyar suka samu raunika a hatsarin motar wanda ya auku a yammacin ranar Juma'a, 1 ga watan Satumba a yankin Olokuta, rahoton PM News ya tabbatar.

Mutum biyu sun halaka a hatsarin mota a Ondo
Rayukan mutum biyu suka salwanta a hatsarin motar Hoto: PMnews.com
Asali: UGC

Mr Ezekiel SonAllah, kwamandan hukumar a jihar ya tabbatar da aukuwar hatsarin ta wayar tarho a ranar Asabar.

Kara karanta wannan

Rashin Daraja: Matashi Ya Halaka Mahaifinsa Mai Shekara 100, Kan Wani Abu 1 Rak Da Ya Yi Masa

SonAllah, wanda ya yi bayanin cewa hatsarin ya auku ne da misalin ƙarfe 5:48 na yamma, ya bayyana cewa hatsarin ya ritsa da maza shida da mace ɗaya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda hatsarin ya auku

Kwamandan ya ɗora alhakin hatsarin wanda ya ritsa da wata motar haya da wata motar ƙirar Toyota Accord, kan gudu wanda ya wuce ƙa'ida.

A kalamansa:

"A ranar Juma'a da misalin ƙarfe 5:48 na yamma kusa da gidan gyaran hali na Olokuta kan titin hanyar Akure-Ondo, wata motar haya ƙirar Nissan Primera mai lamba FGB-96XA da wata mota ƙirar Honda Accord mai lamba MUS-834 AL sun yi hatsari."
"Maza biyu sun rasu a wajen da hatsarin ya auku yayin da wasu maza hudu da mace ɗaya suka samu raunika."
An ajiye gawarwakin mutum biyun da suka rasu a asibitin ƙwararru na Akure, yayin da aka miƙa motocin zuwa hannun ƴan sanda."

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Rayuka Da Dama Sun Salwanta Bayan Wani Gini Ya Rufto Kan Yan Gudun Hijira a Borno

SonAllah ya yi kira ga masu ababen hawa da su riƙa bin dokokin tuƙi inda ya bayyana cewa za a cafke tare da tuhumar duk wanda aka kama yana saɓa dokokin.

Wata Mata Ta Jefa Jaririnta Cikin Kogi

A wani labarin kuma, wata mata ta jefa jaririnta sabuwar haihuwa cikin kogi a jihar Legas, inda ta ce ta gaji da duniya.

Wani bawan Allah ya yi ta maza ya shiga kogin ya ceto jaririn wanda mahaifiyarsa ta nemi salwantar masa da rayuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng