Gwamnatin Zamfara Ba Ta Yi Umurnin Sakin Matan Yan Bindiga Ba - Kwamishina

Gwamnatin Zamfara Ba Ta Yi Umurnin Sakin Matan Yan Bindiga Ba - Kwamishina

  • Gwamnatin jihar Zamfara ta karyata rade-radin da ake yi cewa ta ba da umurnin sakin matan yan bindiga da wasu matasa suka kama
  • Wani mamba a majalisar zartarwa na jihar, Kabir Moyi, ya ce karya ne Gwamna Dauda Lawal bai nemi a sake su ba
  • Ya ce tun farko ma dai gwamnan baya goyon bayan tattaunawa da yan bindigar balle har ya nemi a sako masu mutanensu alhalin suna rike da mutum shida a hannunsu

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Zamfara - Wani kwamishinan jihar Zamfara, Kabir Moyi, ya yi watsi da ikirarin cewa gwamnan jihar, Dauda Lawal Dare, ya bayar da umurnin sakin matan wasu yan bindiga biyu.

Gwamnan Zamfara ya karyata batun ba da umurnin sakin matan yan bindiga
Gwamnatin Zamfara Ba Ta Yi Umurnin Sakin Matan Yan Bindiga Ba - Kwamishina Hoto: @Kdankasa
Asali: Facebook

Gwamnan Zamfara bai yi umurnin sakin matan yan bindida ba, Kwamishina

Moyi ya ce ba gaskiya bane cewa gwamnan jihar ya yi umurnin sakin matan Fulanin, kamar yadda ake ta yayatawa, jaridar Nigerian Tribune ta rahoto.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Tashin Hankali Yayin da Yan Bindiga Suka Farmaki 'Rukunin Gidajen El-Rufai', Sun Sace Wani Mutum

Ya ce:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Ba zai taba yiwuwa ba; ta yaya gwamnan wanda yake adawa da tattaunawa da wadannan yan ta'adda zai yi umurnin sakin matansu, alhalin mazajensu na tsare da mutane shida a hannunsu? Wannan ba gaskiya bane."

Moyi ya jaddada cewar gwamnatin jihar bata da masaniya kan ko an kama matasan da ke rike da matan Fulanin, yana mai cewa za a binciki lamarin.

Jaridar Vanguard ta dai rahoto cewa an samu tashin hankali akauyen Birnin Magaji na jihar Zamfara, bayan wani basarake ya tilasta matasan da suka cafke matan yan bindiga sun saki matan.

Matasa sun yi garkuwa da matan yan bindiga a Zamfara

An tattaro cewa matasa a garin sun kama matan yan bindigar sannan suka sha alwashin kin sakinsu har yan yan bindigar sun saki mutanen garin guda shida da ke tsare a hannunsu.

Kara karanta wannan

Kishi: Wani Matashin Saurayi Ya Buga Wa Budurwarsa Guduma Har Lahira Kan Abu 1

Kwatsam, sai aka ci cewa an bukaci matasan da su saki matan bisa umurnin Sarkin Birnin Magaji. Yayin da wata majiya kuma ta zargi gwamnan jihar da bayar da umurnin sakinsu.

Sai dai kuma, daga majalisar masarautar har gwamnatin jihar sun yi martani a lokuta daban-daban.

Yayin da ba a samu jin ta bakin mai martaba Alhaji Ussaini Magaji ba, sakataren masarautar ya ce za su yi martani kan lamarin a lokacin da ya kamata.

Gwamnatin jihar ta nesanta kanta daga lamarin sannan ta ce za ta yi bincike a kai.

Yan bindiga sun kai hari rukunin gidajen Abuja, sun sace wani

A wani labarin, mun ji cewa mazauna yankin Kuchiko Resettlement Development Area (KRDA) da ke Bwari sun koka kan yawan sace-sacen mutane a cikin yankin.

Hakan ya biyo bayan lamarin da ya afku baya-bayan nan a safiyar Asabar, 2 ga watan Satumba, a yankin da aka fi sani da rukunin gidajen El-Rufai wato ' El-Rufai Estate'.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng