Yadda Yan Bindiga Suka Bindige Masallata a Masallacin Kaduna

Yadda Yan Bindiga Suka Bindige Masallata a Masallacin Kaduna

  • Yan bindiga sun kai kazamin hari kan al'umma a kauyen Saya-Saya da ke yankin Ikara ta jihar Kaduna
  • Maharan sun farmaki wani masallaci ana tsaka da sallar Isha'i inda suka kashe bayin Allah
  • An kashe mutum biyar a cikin masallaci, yayin da aka tsinci gawar wasu biyu a wurare daban daban a yankin

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Kaduna - Wasu da ake zaton yan bindiga ne sun farmaki masallata a wani masallaci a kauyen Saya-Saya da ke karamar hukumar Ikara ta jihar Kaduna, inda suka kashe mutum bakwai.

An bindige mutum biyar a cikin masallacin, yayin da aka tsinci gawarwakin sauran mutanen biyu a wasu wurare daban-daban a cikin yankin, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Yan bindiga sun farmaki masallata a Kaduna
Yadda Yan Bindiga Suka Bindige Masallata a Masallacin Kaduna Hoto: Senator Uba Sani
Asali: Facebook

Yadda yan bindiga suka kashe masallata a masallaci

Kamar yadda majiyoyi suka bayyana, lamarin ya afku ne da misalin karfe 8:00 na dare lokacin da al'ummar kauyen ke sallar Isha'i a wani masallacin yankin.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Tashin Hankali Yayin da Yan Bindiga Suka Farmaki 'Rukunin Gidajen El-Rufai', Sun Sace Wani Mutum

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wani mazaunin kauyen, Dan Asabe, ya ce an kwashi wasu mazauna kauyen biyu da suka ji rauni sakamakon harbi zuwa asibiti don samun kulawa.

Hakimin kauyen, Malam Abdulrahaman Yusuf, ya tabbatar da faruwar lamarin, cewa shugaban yan banga a kauyen na cikin wadanda aka kashe a cikin masallacin.

Ya ce:

"Muna zargin sun bi sahun sa (shugaban yan bangar) zuwa masallacin don farmakar shi. Muna cikin masallacin muna sallah lokacin da suka iso sannan suka fara harbi. An kashe mutane biyar a cikin masallacin, yayin da aka kuma kashe wani direba da ya kawo kayan abinci kauye. Sauran mutum dayan an kashe shi ne a wani kauye da ke kusa."

Ya ce hukumomin tsaro da suka hada da sojoji da yan sanda daga garin Ikara da yankin Palgore sun isa wajen da misalin 12:30 na dare amma zuwa lokacin, yan bindigar sun riga sun bar kauyen.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu Ta Jero Dabarun da Za Ta Bi Domin Gyara Tattalin Arzikin Najeriya

A cewarsa, an dauki daya daga cikin mutanen da suka ji rauni zuwa asibitin Aminu Kano don samun kulawar likitoci.

Ya ce al'ummar kauyen sun shiga rudani.

Rundunar yan sanda ta yi martani

Da aka tuntube shi, babban sakataren labaran Gwamna Uba Sani, Mohammad Lawal Shehu, ya ki yi martani, cewa zai tabbatar da lamarin daga ma'aikatar tsaron cikin gida.

Mukaddashin jami'in hulda da jama'a na rundunar yan sandan jihar, Mansir Alhassan, wanda ya tabbatar da lamarin, ya ce an tura jami'an tsaro zuwa jejin da ke kusa don tsamo masu laifin.

A cewarsa, yan sanda da sauran hukumomin tsaro basu samu labarin harin ba har sai bayan da maharan suka bar yankin.

Ya bukaci jama'a da su dunga kawo rahoton duk wani motsi da basu aminta da shi ba a cikin garuruwansu ga hukumomin tsaro mafi kusa a lokacin da ya kamata.

Wasu Matasa Sun Yi Garkuwa Da Matan 'Yan Bindiga A Jihar Zamfara

Kara karanta wannan

'Kudin Ya Yi Yawa': Ran Majalisa Ya Baci Kan Wasa Da Kudade Na Dashen Itatuwa A Arewacin Najeriya, Ta Fara Bincike

A wani labari na daban, mun ji cewa yayin da 'yan bindiga su ka addabi yankunan jihar Zamfara, mutane sun gano salon ramawa.

Wasu mutane sun yi garkuwa da matan 'yan bindiga a yankin Birnin Magaji da ke jihar Zamfara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng