Kayan Tallafi: Gwamnan Arewa Zai Kashe Biliyan 3.7 Wajen Siyawa Al’ummar Jihar Shinkafa Da Kayan Hatsi
- Gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu Sokoto, ya amince da sakin kudi domin siyan kayan abinci da za a rabawa al'ummar jihar
- An dauki wannan matakin ne a kokarin da gwamnati ke yi na ragewa al'umma radadin cire tallafin mai da aka yi a kasar
- Za a siya shinkafa, gero da masara da kudinsu ya kai naira biliyan 3.7 don rabawa mutane a fadin jihar Sokoto
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Sokoto - Gwamnatin jihar Sokoto ta ware kudi kimanin naira biliyan 4 don siyan kayan abinci da za a raba a fadin kananan hukumomin jihar.
Kamar yadda jaridar Punch ta rahoto, wannan na daga cikin kokarin da gwamnatin jihar ke yi don ragewa al'ummar jihar radadin cire tallafin man fetur.
Gwamnan Sokoto ya amince da siyan kayan abinci don ragewa al'umma radadi
Da yake jawabi ga manema labarai a zauren majalisa bayan taron majalisar zartarwa na jihar a ranar Juma'a, 1 ga watan Satumba, kwamishinan harkokin addini, Sheikh Dr Jabir Maihula, ya ce gwamnan jihar, Ahmed Aliyu Sokoto, ya amince da siyan kayayyaki don rabawa.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A cewar kwamishinan:
"Mambobin majalisar zartarwa na jihar a taronsu sun amince da siyan buhuhunan shinkafa yan 50kg guda 57,000 kan kudi naira biliyan 2.508.
"Majalisar ta kuma amince da siyan wasu buhuhunan gero yan 100kg guda 26,000 kan kudi naira biliyan 1.430."
Ya ce kayayyakin sun hada da buhuhunan masara 44,000 wanda gwamnatin tarayya za ta siya da hadin gwiwar gwamnatin tarayya, rahoton Nigerian Tribune.
Ya yi bayanin cewa gwamnan ya kafa wani kwamitin da zai kula da rabon kayan abinci a fadin kananan hukumomi 23 na jihar.
Ikon Allah: Gwamnan Arewa Ya Lale Kudi Sama da Biliyan Ɗaya Ya Siyo Motoci 10 Domin Taimaka Wa Talakawa
Gwamnati ta ware biliyoyi don siyan motocin da zai dunga jigilar mutane
A halin da ake ciki, domin saukakawa mutane zirga-zirgan ababen hawa, majalisar dokokin jihar ta kuma amince da siyan motoci masu zaman mutum 18 guda 50, samfurin 2022 a kan naira biliyan 2.8.
Ta kuma ware sama da miliyan 560 don siyan motocin Toyota Camry sumfurin 2022 guda 20, domin jigilar mata a jihar.
Kwamishinan ya kuma bayyana cewa za a hada motocin da wasu bas 10 da rukunin kamfanin BUA ya bayar tallafi a kwanan nan.
Gwamnan Neja ya ba da hutun kwana 3 don rabon kayan tallafi
A wani labari makamancin wannan, mun ji cewa gwamnan jihar Neja, Mohammed Umar Bago, ya ayyana ranar Laraba, 6 ga watan Satumba, zuwa Juma'a, 8 ga watan Satumba a matsayin hutu a fadin jihar.
Kamar yadda jaridar The Nation ta rahoto, Bago ya ce an bayar da hutun ne domin rabon kayan tallafi a jihar don ragewa al'umma radadin cire tallafin man fetur.
Asali: Legit.ng