Zan Bayyana Masu Hannu a Kashe-Kashen Rayuka Nan Da Mako Guda, Gwamna Uzodinma
- Gwamna Uzodinma na jihar Imo ya lashi takobin bayyana masu ɗaukar nauyin kashe-kashen mutane a jihar
- Shugaban ƙungiyar gwamnonin jam'iyyar APC ya nanata cewa matsalar tsaron jiharsa siyasa ce kuma masu kitsa lamarin sun san kansu
- Ya ce ba zai naɗe hannu yana kallo ana kashe mambobin jam'iyyarsa ta APC ba, zai yi maganin duk wani mai hannu
Imo - Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma, ya sha alwashin ganin bayan masu rura wutar rashin tsaron da ya addabi jihar da ke Kudu maso Gabashin Najeriya.
Uzodinma, shugaban gwamnonin jam'iyyar APC mai mulki ya ce nan da mako ɗaya, zai tona asirin masu ɗaukar nauyin kashe-kashen rayuka a jihar Imo.
Gwamnan ya bayyana haka ne a cikin shirin Siyasa a Yau a gidan talabijin na Channels tv ranar Jumu'a, 1 ga watan Satumba, 2023.
A kalamansa, gwamna Uzodinma ya ce:
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
"Nan da 'yan makonni masu zuwa, abinda zamu yi, zamu fallasa dukkan masu ɗaukar nauyin kashe-kashen rayuka da matsalar tsaron da ta addabi jihar Imo."
Gwamnan ya jima yana nanata cewa wannan rashin tsaro da ƙaruwar ayyukan ta'addanci a jiharsa yana da alaƙa da siyasa.
Wane matakin gwamnan zai ɗauka na gaba?
Amma da aka tambaye shi yiwuwar bayyana masu rura wutar matsalar tsaron, Mista Uzodinma ya sha alwashin dawo da zaman lafiya, yana mai cewa tuni ya umarci hukumomin tsaro su bankaɗo masu ɗaukar nauyi.
Haka zalika gwamna Uzodinma ya yi ikirarin cewa akasarin wadanda aka kashe mambobi ne a gwamnatinsa.
A rahoton The Cable, ya ƙara da cewa:
“Na nemi jami’an tsaro su gaya mani dalilan da suka haddasa hakan. Ba wai tsautsayi ba ne a ce yawancin mutanen da ake kashewa ‘yan jam’iyyata ne ta APC."
“A ‘yan kwanakin nan, jiga-jigan ‘yan jam’iyyata da suka halarci zaben da ya gabata, ana kai wa gidajensu hari. Wasu sarakunan gargajiya da suka tausaya wa jam’iyyarmu, suma sun shiga matsala."
“Ina rokon wadanda suke da hannu a kashe-kashe a jihar Imo, da garkuwa da mutane da sunan siyasa da su daina. Na faɗa ba sau ɗaya ba cewa matsalar tsaro a Imo siyasa ce, kuma masu ɗaukar nauyin sun san kansu."
Fitacciyar Malamar Addini Ta Gane Gaskiya, Ta Karɓi Addinin Musulunci
A wani labarin kuma Shahararriyar mai bin addinin gargajiyar nan a jihar Kwara, Iya Osun ta furta kalmar shahada, ta koma Musulunci.
A wani Bidiyo da ke yawo, Iya Osun ta bayyana cewa ta karɓi addinin Musulunci ne bisa ra'ayin kanta, babu wanda ya tilasta mata.
Asali: Legit.ng