Abun Farin Ciki Yayin da Gwamnan Arewa Ya Ayyana Hutun Kwana 3, Ya Fadi Dalili

Abun Farin Ciki Yayin da Gwamnan Arewa Ya Ayyana Hutun Kwana 3, Ya Fadi Dalili

  • Gwamnatin jihar Neja ta ayyana hutun kwana uku a fadin kananan hukumomin jihar
  • Gwamna Mohammed Umar Bago, wanda ya sanar da hakan ya ce an ba da hutun ne domin raba kayan tallafi
  • Bago ya bayyana cewa za a raba kayan tallafin ne a rumfunan zabe da kuma matakin gudunma

Jihar Niger - Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umar Bago, ya ayyana ranar Laraba, 6 ga watan Satumba, zuwa Juma'a, 8 ga watan Satumba a matsayin hutu a fadin jihar.

Kamar yadda jaridar The Nation ta rahoto, Bago ya ce an bayar da hutun ne domin rabon kayan tallafi a jihar don ragewa al'umma radadin cire tallafin man fetur.

Bago ya ba da hutun kwana uku don raba kayan tallafi a jihar Neja
Abun Farin Ciki Yayin da Gwamnan Arewa Ya Ayyana Hutun Kwanaki 3, Ya Fadi Dalili Hoto: Mohammed Umar Bago
Asali: Facebook

An ba da hutu don rabon kayan tallafi

Gwamnan ya sha alwashin tura duk wanda aka kama ya karkatar da kayan tallafi ko kudin da ya kamata a siya kayan zuwa gidan yari.

Kara karanta wannan

Tsadar Fetur: Yadda Abba Gida Gida Ya Yi Rabon Kayan Tallafi ga Mata da Manoma

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya bayyana hakan ne a taron manema labarai a gidan gwamnati da ke Minna, babban birnin jihar, rahoton Nigerian Tribune.

Za a yi rabon ne a rumfunan zabe da matakin gudunma

Ya yi bayanin cewa za a yi rabon tallafin ne a rumfunan zabe da matakin gudunma.

Bago ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta karbi naira biliyan 2 a matsayin tallafin kudi da manyan motoci biyar na shinkafa daga gwamnatin tarayya.

Ya kara da cewa saura naira biliyan 3 da buhuhunan masara 40,000 da ake sa ran samu daga gwamnatin tarayya.

Jihar za ta kara Naira miliyan 230 kan Naira biliyan 5 da gwamnatin tarayya za ta bayar.

"Za a rabawa kowace gudunma a kananan hukumomi 21 miliyan 10 yayin da gudunmomi a kananan hukumomin Bida, Suleja, Kontagora da Chanchaga za su samu miliyan 20 kowannensu. naira miliyan 80 zai tafi bangaren sarautar gargajiya don kada su yi wadaka da abun da ya kamata a bai wa mutane, naira miliyan 75 ga yan gudun hijira, naira miliyan 150 ga jam'iyyun siyasa don kada su karkatar da kayan ta;;afin, sannan naira miliyan 110 na kayan aiki da tsaro.

Kara karanta wannan

"Babu Dawowa Baya", Kashim Shettima Ya Tona Asirin Shirin Masu Handame Kudaden Tallafi, Ya Tura Gargadi

"Za a rabawa raba kudaden zuwa asusun kananan hukumomi a ranar Litinin. Ya zama dole kowa ya zauna a gudunma da karamar hukumarsa. Ba dole sai shinkafa za ku siya ba. Idan mutanenku sun saba da cin wake ko doya, ku siya masu. karamar hukuma da gudunmomi ne za su yanke shawara kan abun da za su siya. Mun yanke shawarar cewa ba za mu karkasa wannan kudi ba domin mu mayar da dukiyar ga jama’a.”

Legit.ng ta tuntubi wata mazauniyar garin Minna a jihar Neja don jin yadda rabon kayan tallafin ya kaya a wajensu.

Matar da ke zaune a unguwar Brighter da ke garin Minna ta ce sam basu ma san an yi wani rabo ba.

Ta ce:

“Mu dai abun bai iso wajenmu ba a unguwar mu ban ga ko mutum daya da yace mun ya samu wannan kayan tallafi ba balle har ya kai hannuna. Akwai dai wata da muke mutunci da ita a yankin Chancaga da tace mun taliya daya aka bai makwabciyarta. Shin me taliya daya za ta yi wa mutum a wannan marra da ake ciki.

Kara karanta wannan

Kwanaki 100 Kan Mulki: Tarun Matsaloli 3 Da Ke Hana Shugaba Tinubu Sakewa Tun Bayan Hawanshi Mulki

“Gaskiya ina ganin ba a bi hanyar da ta dace wajen rabon ba. Da kamata ya yi ace tunda babban bankin kasar na da lambar asusun kowa kawai da tura kudin aka yi mana kai tsaye. Watakila da abun ya iso garemu amma dai mu ba mu gani a kasa ba.

Cire Tallafi: Gwamnatin Tinubu Ta Tura Wa Jihohi Biliyan 2 Maimakon Biliyan 5

Da farko Legit.ng ta rahoto cewa gwamnatin tarayya ta tura wa kowace jiha Naira biliyan 2 ne kaɗai daga cikin Naira biliyan 5 da ta amince zata bai wa jihohi a matsayin tallafi domin rage tasirin cire tallafin man Fetur.

Gwamnatin karƙashin jagorancin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ta sakar wa kowace jiha Naira biliyan 2 ne domin daƙile hauhawar farashin kayayyaki idan ta saki N5bn.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng