Matakan Shugaba Tinubu Sun Fara Dawo da Zaman Lafiya a Zamfara, Inji Yari
- Tsohon gwamnan Zamfara, Sanata Abdul'azizi Yari ya ce kyawawan ayyukan Tinubu sun fara dawo da zaman lafiya a jihar
- Yari, Sanata mai wakiltar Zamfara ta yamma ya ce haƙar ma'adanai ba bisa ƙa'ida ba yana da alaƙa da rashin tsaron da ake fama da shi
- Ya ce shugaban ƙasa ya fara ɗaukar matakai kuma ko a yanzu an fara ganin ci gaba a sha'anin tsaron jihar Zamfara
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
FCT Abuja - Sanata mai wakiltar Zamfara ta yamma, Abdulaziz Yari, ya ce kyakkyawan ayyukan da shugaban kasa Bola Tinubu ke yi ya fara dawo da zaman lafiya da tsaro a jihar.
Vanguard ta ce Yari, tsohon gwamnan Zamfara, ya yi wannan furucin ne yayin hira da 'yan jarida ranar Alhamis bayan ya ziyarci Tinubu a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Ya ce ayyukan haƙar ma'adanai ba bisa ƙa'ida ba ne ke haddasa sace-sacen shanu da garkuwa da mutane a jihar Zamfara, wanda a yanzu suka zama babbar barazana ga tsaro.
Ya ce tura jami’an tsaro da shugaban ya yi ya fara haifar ta ɗa mai ido a ƙoƙarin dawo da zaman lafiya a yankunan da ‘yan bindiga suka addaba, kamar yadda The Cable ta rahoto.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Yari ya faɗi abinda ke haddasa rashin tsaro
Sanata Yari ya ce:
"Lokacin ina gwamna, ban yarda cewa haƙar ma'adai na ɗaya daga cikin tushen matsalar ba, amma bayan na sauka sai na fara lura cewa akwai dangantaka tsakanin matsalar tsaro da haƙar ma'adanai."
“Shekara daya bayan na sauka, wasu kungiyoyi sun yi zanga-zanga a karamar hukumar Kaura Namoda, inda suka ce ba su fahimci dalilin da ya sa muke cewa babu wata alaka tsakanin rashin tsaro da haƙar ma’adinai."
"Kusan kowace rana za a kai wa mutanen ƙauyuka hari, yayin da mutanen da ke aikin hakar ma’adinai suna zaune lafiya, ba abinda yake samun su."
“Amma na gane cewa ma’adanai da rashin tsaro suna da dangantaka kuma na yi imanin Tinubu na yin iya kokarinsa domin ya fara tattaunawa da mai ba shi shawara kan tsaro game da batun kuma an samu ci gaba sosai."
Shugaba Tinubu Ya Tura Wa Kowace Jiha N2bn Maimakon N5bn
A wani rahoton na daban Gwamnatin shugaba Tinubu ta sakar wa kowace jiha a Najeriya Naira biliyan 2 maimakon biliyan N5 na rage radaɗin cire tallafin fetur.
Ministan kuɗi na tarayya, Wale Edun, ya ce FG ta yi haka ne domin kauce wa tashin farashin kayayyakin idan ta saki kuɗin baki ɗaya.
Asali: Legit.ng