Jami'an Tsaro Sun Kama Matashi Kan Zargin Kisan Mahaifinsa A Jihar Ogun
- Jami'an tsaro a jihar Ogun sun kama wani matashi mai shekaru 20 kan zargin kisan mahaifinsa
- Wanda ake zargin mai suna Ridwan ya tabbatar da kisan mahaifin nasa don neman abin duniya
- Yayin bincike, ya tabbatar da cire al'auran mahaifin nasa da hakora guda hudu da sauran bangarori
Jihar Ogun - An kama wani matashi mai shekaru 20 a jihar Ogun kan kisan mahaifinsa saboda kudin asiri.
Wanda ake zargin mai suna Ridwan an kama shi ne a kauyen Oshoku da ke karamar hukumar Ijebu ta Arewa a jihar.
Meye matashin ya aikata a Ogun?
Kwamandan jami'an tsaron So-Safe Corps, Soji Ganzallo a cikin wata sanarwa da kakakin hukumar ya fitar, Yusuf Moruf ya ce sun kama Ridwan yayin rangadi.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Yusuf ya ce lokacin da su ke Oshoku sun ji wani kara yayin da su ka garzaya wurin don sanin meye ya ke faruwa, Daily Trust ta tattaro.
Ya ce jami'ansu sun shiga wani gida inda su ka tarar da gawa kwance cikin jini da alamu wanda ya yi kisan ya tsere.
Ganzolla ya umarci kwamandan yanki na Ijebu, Marcus Ayankoya da ya kamo wanda ake zargin cikin sa'o'i 24.
Sanarwar jami'an tsaro kan kama matashin
Ya ce:
"An kama wanda ake zargin a maboyarsa da ke cikin daji.
"Ya bayyana cewa shi ya kashe mahaifinsa Ishau, da igiya wanda ya yi amfani da shi a wuyansa.
"Ya kuma tabbatar da cewa ya yi amfani da wuka wurin cire wasu sassa na jikinsa."
Ridwan ya kara da cewa ya cire al'auran mahaifin nasa da kuma hakora hudu da sauran sassa kamar yadda Baba Kekere ya umarce shi.
Hukumar ta mika shi ga ofishin 'yan sanda na yanki don ci gaba da bincike, cewar Tribune.
Fasto Ya Cinnawa Budurwa Wuta Lokacin Ibada A Ogun
A wani labarin, An kama Fasto Taiwo Odebiyi na Cherubim and Seraphim Church, Maberu Parish wacce ke a Offin a yankin Sagamu na jihar Ogun.
Faston ya shiga hannun jami'an 'yan sanda bisa cinnawa wata budurwa wuta yayin gabatar da addu'a.
Faston dai ya cinnawa budurwar mai suna Sukura Owodunni, mai shekara 21 a duniya wuta ne lokacin da ya ke yi mata addu'a ta musamman.
Asali: Legit.ng