Kungiyar NLC Za Ta Tsunduma Yajin Aiki Na Kwanaki 2 Kan Cire Tallafi
- Kungiyar Kwadago ta NLC ta shirya shiga yajin aiki kan masifar da cire tallafi ya jefa mutane
- Kungiyar ta ce hakan ya zama dole ganin yadda mutane ke cikin mawuyacin hali bayan cire tallafi
- Wannan na zuwa ne bayan shugaban kasar ya ware biliyoyin kudade ga jihohi 36 don rage musu radadin cire tallafi
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
FCT, Abuja - Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) za ta shiga yajin aiki na kwanaki biyu kan cire tallafin mai.
Kungiyar ta ba da wannan sanarwa ce a yau inda ta ce shiga yajin aikin gargadin ya zama dole.
Meye NLC ta ce kan yajin aikin?
NLC ta ce ganin yadda cire tallafin man fetur ya saka 'yan Najeriya a cikin mawuyacin hali shi yasa su ka yanke wannan hukunci, cewar TheCable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ana sa ran kungiyar za ta fara yajin aikin ne a ranar Talata 5 ga watan Satumba na 2023.
Shugaban kungiyar, Joe Ajaero shi ya bayyana haka a yau Juma'a 1 ga watan Satumba a Abuja yayin ganawa da manema labarai.
Ya ce hukuncin na zuwa ne bayan ganawar da kungiyar ta yi da mambobinta a ranar Alhamis 31 ga watan Agusta.
Wane zargi NLC ke yi kan gwamnati?
Kungiyar na zargin Gwamnatin Tarayya da watsi da alkawuran da ta dauka a ganawar da su ka yi a kwanakin baya.
A ranar 2 ga watan Agusta ne kungiyar ta gudanar da zanga-zanga a fadin kasar kan irin tsare-tsaren da gwamnatin ke kawo wa.
NLC ta ce sabbin manufofin gwamnatin sun jefa mutane a kasar cikin mummunan yanayi da kunci, cewar Channels TV.
Kungiyar NLC da takwararta TUC sun gudanar da zanga-zanga a jihohin Najeriya da su ka hada da Legas da Kano da Edo da Katsina da Abia.
Sauran sun hada da Kaduna da Plateau da Rivers da Enugu da Zamfara da Ebonyi da Kwara da Imo da birnin Abuja da sauransu.
NLC Ta Fara Zanga-Zanga Kan Cire Tallafi
A wani labarin, Kungiyar NLC ta fara zanga-zanga a fadin Najeriya don nuna rashin jin dadinta kan cire tallafin mai..
Wannan na zuwa ne bayan gwamnatin Bola Tinubu ta cire tallafin mai a watan Mayu na 2023.
Asali: Legit.ng