Mijina Bai Kwanta Da Ni Ba Tsawon Shekaru 2, Matar Aure Ta Nemi Kotu Ta Raba Su
- Ruqayya Mukhtar, matar aure mai shekaru 25 ta nemi kotu ta raba aurenta da mijinta, Naziru Hamza
- Matar ta yi zargin cewa shekaru biyu kenan rabon mijinta ya kusanceta da sunan auratayya
- Sai dai, Hamza ya karyata zargin nata inda ya ce yana iya bakin kokarinsa wajen biya mata bukatarta amma ita kullun sai ta nemi a tara da ita
Jihar Kaduna - Wata matar aure mai shekaru 25, Ruqayya Mukhtar ta fada ma wata kotun Shari'a da ke Rigasa, jihar Kaduna a ranar Alhamis, 31 ga watan Agusta, cewa mijinta bai kwanta da ita ba tsawon shekaru biyu.
Mai karar wacce ta nemi kotu ta raba aurenta da wani mai Naziru Hamza ta kuma koka cewa mijin nata na cin zarafi da mutuncinta, Daily Nigerian ta rahoto.
"Shi Ya Dauki Nauyin Karatuna": Bayan Shekaru 3 a Turai, Budurwa Ta Dawo Najeriya Don Samun Saurayinta Bakanike, Bidiyon Ya Yadu
Ina iya bakina da matata amma ita kullun sai dai a kusance ta, magidanci
Da yake kare kansa, wanda ake karar ya karyata zargin cewa yana iya bakin kokarinsa don biyawa matarsa bukatarta ta bangaren auratayya.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya ce:
"Tunda ina fita kullun don neman na abinci, Wasu lokutan ina dawowa gida da dare ne kuma a gajiye amma matata bata fahimta, a kodayaushe tana so na kusance ta.
"Na kan amsa mata sau da yawa sannan wasu lokutan na kan roketa ta yi hakuri har zuwa washe gari kuma bana dukanta."
Wane mataki alƙalin kotun ya fara ɗauka?
Alkalin, Anas Khalifa, ya tambayi mai karar ko tana da shaidu kuma ta amsa da eh.
Ya dage sauraron shari'ar har zuwa ranar 5 ga watan Satumba don mai karar ta gabatar da shaidunta.
Wani mutum ya saki matansa uku a rana daya, ya fadi dalili
A wani labari na daban, mun ji cewa wani mutumin kasar Uganda, Mutiatya, ya saki matansa uku a rana daya, inda suka tafi suka barsa da yara bakwai.
Afrimax ta yi hira da mutumin mai shekaru 55, wanda ya ziyarci kasashe 14, sannan ta bayyana dalilin da yasa ya rabu da matansa.
Mutiatya ya ce ya saki matansa saboda munanan halayensu. Ya tuna yadda abubuwa ke tafiya daidai a bayan har zuwa lokacin da ya rasa aikinsa.
Asali: Legit.ng