"Mu Na Daf Da Bankwana Da Rashin Tsaro, Ministan Tsaro, Badaru Ya Magantu
- Sabon ministan tsaron Najeriya, Badaru Abubakar ya sha alwashin kawo karshen matsalar tsaro nan ba da jimawa ba
- Badaru ya ce da zarar gwamnati ta samar da kayan aiki na zamani ga jami'an tsaro to shikenan kasar za ta yi bankwana da rashin tsaro
- Ministan ya bayyana haka ne yayin taron Kungiyar Lauyoyi ta Najeriya, NBA a Abuja inda ya fadi kokarin da su ke na tabbatar da haka
FCT, Abuja - Ministan tsaro a Najeriya, Muhammad Badaru Abubakar ya bayyana cewa Najeriya na daf da bankwana da rashin tsaro da ya mata katutu.
Badaru ya bayyana haka ne yayin taron Kungiyar Lauyoyi ta Najeriya, NBA a Abuja.
Meye Badaru ya ce kan tsaro?
Ya ce idan gwamnati ta samar da kayan aiki na zamani ga jami'an tsaro to ba shakka an kawo karshen rashin tsaro, TheCable ta tattaro.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ministan ya ce hukumar rundunar tsaron kasar ta himmatu wurin mayar da komai na zamani don dakile matsalar tsaro.
Ya kara da cewa a yanzu haka kasar na inganta masana'antun sojoji don kirkirar kayayyaki da kuma rage rashin aikin yi a Najeriya, cewar The Guardian.
Badaru ya bayyana hanyar dakile matsalar tsaro
Badaru wanda ya samu wakilcin Ibrah Kena, sakataren din-din-din na ma'aikatar ya ce:
"Idan aka samar da kayan aiki na zamani, shikenan mun yi bankwana da rashin tsaro a kasar.
"Gwamnati ta himmatu wurin samar da sabbin tsare-tsare da suka hada da 'Falcon Eye' da kuma na arzikin ma'adinai na ruwa.
"Gwamnatin ta zuba makudan kudade a tsare-tsaren don kawo karshen rashin tsaro a Neja Delta da sauran wurare kusa da ruwa."
Wannan na zuwa yayin da 'yan kasar ke cikin mawuyacin hali na matsalar tsaro musamman a yankin Arewa.
Yan Bindiga Sun Shiga Taitayinsu Bayan Nada Matawalle Minista, Kaura
A wani labarin, tsohon mai bai wa karamin ministan tsaro, Bello Matawalle shawara na musamman, Abdullahi Anas Kaura ya ce tun bayan Matawalle a matsayin minista, hakan ya jirkita 'yan ta'adda a Najeriya.
Anas Abdullahi Kaura ya bayyana haka a birnin Kaduna a ranar Lahadi 20 ga watan Agusta inda ya ce hakan zai taimaka wurin dakile matsalar tsaron gaba daya a kasar.
Asali: Legit.ng