Juyin Mulki A Afirka: Abubuwa 5 Da Ya Kamata Ku Sani Kan Gabon Yayin Da Ka Kifar Da Gwamnati

Juyin Mulki A Afirka: Abubuwa 5 Da Ya Kamata Ku Sani Kan Gabon Yayin Da Ka Kifar Da Gwamnati

Libreville, Gabon - Sojijin kasar Gabon a karshe sun yi nasarar kifar da gwamnatin Shugaba Ali Bongo bayan rashin nasarar hakan shekarar a 2019.

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Sojojin sun yi nasarar kifar da gwamnatin ne a yau Laraba 30 ga watan Agusta inda su ka sanar a gidan talabijin kasar.

Juyin mulki a kasar Gabon na zuwa ne makwanni shida da kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum a Nijar.

Sojin kasar Gabon sun soke zaben da aka gudanar a ranar Asabar 26 ga watan Agusta.

Abubuwa 5 muhimmai da ba ku sani ba game da Gabon yayin da aka yi juyin mulki
Abubuwa 5 Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Gabon. Hoto: Itz Ode.
Asali: Facebook

Legit.ng ta jero muku muhimman abubuwa guda 5 game da kasar Gabon:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

1. Rashin nasarar juyin mulki a 2019

Kamar yadda Aljazeera ta ruwaito a 2019 an a samu rashin nasara bayan Laftanar Kelly Ondo Obiang ya sanar da kifar da gwamnati a gidan talabijin.

Kara karanta wannan

Gabon: Faransa Ta Tafka Mummunar Asara Bayan Kaddamar Da Juyin Mulki A Kasar, Bayanai Sun Fito

Obiang ya ayyana kansa a matsayin shugaban tsaron Gabon da kuma mataimakin kwamandan tsaro.

2. Ahalin Bongo na mulki tsawon shekaru 47

Iyalan gidan Bongo na rike da madafun ikon kasar na kusan shekaru 50 tun daga 1967.

Omar Bongo ya mulki kasar tun 1967 har zuwa 2009 da ya rasu, shekaru 47 kenan.

Dan cikinsa, Ali Bongo ya gaji kujerar har zuwa yanzu da aka yi nasarar juyin mulki.

3. Wa'adin shekaru bakwai

Britannica ta tattaro cewa a sabon tsarin mulki da aka yi wa gyara, shugaban kasar Gabon zai yi wa'adin shekaru bakwai a kan mulki.

Shugaban kasa a Gabon na da karfin ikon da zai rusa majalisar Tarayyar kasar.

4. 'Yancin kai

Gabon da ke Nahiyar Afirka ta Tsakiya ta samu 'yancin kanta a hannun Faransa a ranar 17 ga watan Agusta 1960.

Allah ya albarkaci kasar Gabon da yawan jama'a har miliyan 2.4.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Bikin Murna Ya Barke a Gabon Yayin da Sojoji Suka Karbe Mulki Daga Shugaban Kasa Ali Bongo, Hotuna Sun Bayyana

5. Iyaka

Gabon ta hada iyaka da Equatorial Guinea da Kamaru daga Arewa sai Congo daga Gabas da Kudu.

Sojoji Sun Kifar Da Gwamnatin Gabon

A wani labarin, rundunar sojin kasar Gabon a safiyar yau Laraba 30 ga watan Agusta sun kifar da gwamnatin Ali Bongo.

Wannan na zuwa ne bayan kammala zaben shugaban kasar a ranar Asabar 26 ga watan Agusta.

Ali Bongo ya shafe shekaru 12 ya na mulkin kasar tun bayan mutuwar mahaifinsa a shekarar 2009.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.