Mutumin Da Ya Kirkiri Tutar Najeriya, Pa Taiwo Akinkunmi Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

Mutumin Da Ya Kirkiri Tutar Najeriya, Pa Taiwo Akinkunmi Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

  • Pa Michael Taiwo Akinkunmi (OFR), mutumin da ya kirkiri tutar Najeriya ya riga mu gidan gaskiya
  • Allah ya yi wa dattijon mai shekaru 84 rasuwa a ranar Talata, 29 ga watan Agusta, bayan ya yi fama da rashin lafiya
  • Marigayin ya shiga gasar kirkirar tutar Najeriya kuma ya yi nasara lokacin yana da shekaru 23 a duniya

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Allah ya yi wa mutumin da ya kirkiri tutar Najeriya, Pa Michael Taiwo Akinkunmi (OFR), rasuwa.

Pa. Akinkunmi, mai shekaru 84 ya mutu a safiyar ranar Talata, 29 ga watan Agusta, bayan yar gajeruwar rashin lafiya.

Daya daga cikin 'ya'yan marigayin ne ya sanar da labarin mutuwar nasa kamar yadda jaridar Nigerian Tribune ta rahoto.

Pa Taiwo Akinkunmi wanda ya kirkiri tutar Najeriya ya rasu
Mutumin Da Ya Kirkiri Tutar Najeriya, Pa Taiwo Akinkunmi Ya Riga Mu Gidan Gaskiya Hoto: @NTANewsNow
Asali: Twitter

Ya bayyana cewa shakka babu rayuwa mai shudewa ce amma mahaifinsu ya bar abun da ba za a manta da shi ba.

Kara karanta wannan

Ibrahim Geidam: Muhimman abubuwa 6 da baku sani ba game da ministan harkokin 'yan sanda

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya ce:

“Hakika rayuwa mai shudewa ce; Zan iya fadi cike da kwarin gwiwa cewa kayi rayuwa mai dumbin tarihi. Ci gaba da hutawa mahaifina! Pa Michael Taiwo Akinkunmi (O.F.R.): Babban Mutum ya tafi."

Takaitaccen tarihin mutumin da ya kirkiri tutar Najeriya

Marigayi Akinkunmi ya kasance haifaffen dan Abeokuta a jihar Ogun. An haife shi a ranar 10 ga watan Mayun 1939. Ya yi rayuwarsa a Ibadan, babban birnin jihar Oyo.

Marigayin ya yi karatunsa na Firamare a Baptist Day Secondary School, Ibadan. Ya kuma yi karatunsa na sakandare a Ibadan Grammar School.

Dattijo Akinkunmi ya na da shekaru 23 a duniya lokacin da ya shiga gasar kirkirar tutar Najeriya kuma ya samu kyautar kudi fan 100 (Dala 281) da kuma samun matsuguni cikin kundin tarihin Najeriya sakamakon nasarar da ya samu.

Kara karanta wannan

Ana Mulkin 'Yan Koyo: Shehu Sani Ya Jero Wadanda Ya Kamata Tinubu Ya Nada Ministoci

Allah ya yi wa mahaifiyar Abba El-Mustapha rasuwa

A wani labari makamancin wannan, mun ji cewa masana'antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood ta shiga juyayi da alhini yayin da mahaifiyar shugaban hukumar tace fina-finai ta jihar Kano kuma babban jarumi, Abba El-Mustapha ta rasu.

El-Mustapha da kansa ne ya sanar da labarin mutuwar mahaifiyar tasa wacce ya kira da Gwagwgo a ranar Talata, 29 ga watan Agusta.

Da yake nuna alhinin wannan babban rashi da ya yi a shafinsa na Instagram, shugaban hukumar tace fina-finan ya bayyana cewa ya rasa duniyarsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng