Zagayowar ranar samun 'yanci: Tarihin mutumin da ya kirkiri tutar Najeriya da ma'anar kalolin jikinta

Zagayowar ranar samun 'yanci: Tarihin mutumin da ya kirkiri tutar Najeriya da ma'anar kalolin jikinta

- A bikin cikar Najeriya shekaru 58 da kafuwa a matsayin kasa mai 'yanci, wadda aka faro tun 1914, sai gashi an samo wanda ya hado tutar kasar nan da ransa

- Hira da Aljazeera ta bashi damar fadin yadda yayi tunanin tutar, launin ta da ma'anar ta

- Har yanzu yana raye, kuma kai baka ce ya sami wata muhimmiyar dukiya ya tara ba

Michael Taiwo Akinkunmi yana karatu injiniya ne a 'Norwood Technical College London' dake kasar Ingila a shekarar 1959, kuma yana da shekarun haihuwa 23 lokacin da ya shiga gasar kirkirar tutar Najeriya kuma daga bisani yayi nasara har ya samu kyautar kudi fan 100 (Dala 281) a shekarar 1959 da kuma samun matsuguni cikin kundin tarihin Najeriya.

Tarihin tutar Najeriya da ma'anar kalolon jikinta
Tutar Najeriya
Asali: Facebook

Mista Akinkunmi na rayuwa ne yanzu a matsayin dan fansho a garin Ibadan a gidansa dake cikin unguwar talakawa inda ko hanyar mota babu. Akinkunmi yace tafiya mai tsawo da yayi tun bayan da ya bar aiki, ita ce zuwa Abuja a shekarar 2014 lokacin da tsohon shugaban kasa Jonathan ya karrama shi tare da kirkirar masa albashin dundundun na naira dubu 800, Wanda yace duk wata ana biyan shi har yanzu.

DUBA WANNAN: Samun ‘yanci: Hotuna daga bikin cikar Najeriya shekaru 58

Akinkunmi yanzu haka na fama da matsalar mantuwa domin yace bazai iya tuna mai tsohon shugaban kasa Jonathan ya fada masa ba lokacin da ya gayyace shi, hakazalika ya kasa tuna sunayen abokansa na kuruciya, hasali ma dai bai iya fadin sunan makarantar da yayi a Ingila daidai ba, sannan ya kasa tuna dalilin da yasa akayi masa tiyata jim kadan bayan ya bar aiki a shekarar 1993.

Akinkunmi yanzu haka nada shekara 80 na haihuwa kuma fentin gidansa kore da fari ne kamar yadda yayi fentin tutar Najeriya. Ya ce kalar tutar na nufin noman mu, arzikinmu, mutuncin mu, da kimar mu a idon duniya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel