Fani-Kayode Ya Yi Martani Kan Juyin Mulkin Gabon, Ya Ce Bai Kamata A Yi Mamakin Hakan Ba
- Yayin da ake faman neman sulhu tsakanin sojin kasar Nijar da kungiyar ECOWAS, an sake juyin mulki a Gabon
- Sojoji a kasar Gabon sun bayyana haka a gidan talabijin na kasar inda su ka sanar da rusa zaben da aka gudanar
- Jigo a jam'iyyar APC, Femi Fani-Kayode ya yi martani kan juyin mulkin inda ya ce bai kamata mutane su yi mamaki ba don ya san haka za ta faru
FCT, Abuja - Tsohon minista a Najeriya, Femi Fani-Kayode ya ce bai yi mamakin juyin mulki ba da aka yi a kasar Gabon.
Fani-Kayode wanda aka fi sani da FFK ya ce kasashen Afirka ta Yamma da Tsakiya za su fi fuskanci irin wannan matsalar, Legit.ng ta tattaro.
Meye Fani-Kayode ya ce kan juyin mulkin Gabon?
FFK ya ce kasashen da su ka fi hatsarin samun juyin mulki su ne wadanda ke karkashin kasar Faransa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Jigon jam'iyyar APC, ya bayyana haka ne a shafinsa na Twitter inda ya bayyana hasashen da ya yi gaskiya ne.
Ta ce:
"Gargadin da na bayar a baya ashe ya tabbata inda na ce "Shin kisan jarirai da ke Nijar zai kawo mana nasara.
"Ban yi mamakin faruwar hakan ba, kuma gaskiya mu yi tsammanin karin faruwar hakan musamman kasashen Afirka ta Yamma da Tsakiya karkashin Faransa.
"Ina mamakin ko ECOWAS da AU za su yi barazanar mamayar kasar Gabon."
Meye sojoji su ka yi a kasar Gabon?
Rahotanni sun tabbatar da cewa sojin kasar Gabon sun tabbatar da soke zaben shugaban kasa da aka yi a kasar tare da rushe dukkan hukumomin gwamnati.
Hambararren shugaban kasar Gabon, Ali Bongo ya shafe shekaru 12 ya na mulki tun bayan mutuwar mahaifinsa a shekarar 2009.
Wannan juyin mulki ya kawo karshen mulkin shekaru 53 na ahalin gidan Bongo da su ka kwashe su na mulkin kasar.
Jerin Kasashen Afirka 7 Da Ke Karkashin Mulkin Soja
A wani labarin, kasashen Afirka ta Yamma sun fi fuskantar matsalolin juyin mulki tun bayan dawowar dimukradiyya.
Wannan na zuwa ne bayan sojoji sun kifar da gwamnatin Ali Bongo a kasar Gabon bayan rushe zaben da aka gudanar.
Asali: Legit.ng