Gwamnatin Tinubu Zata Dauki Mutane 300,000 Aiki a Hukuma Daya Tilo
- Gwamnatin tarayya zata ɗauki sabbin ma'aikata 300,000 a sabuwar hukumar dakile yaɗuwar makamai (NATCOM)
- Muƙaddashin shugaban hukumar, Otunba Adejare Rewane, ya ce za a ɗauki mutane 7,000 a kowace jiha da kuma Abuja
- Wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da matsalar tsaro ke ƙara taɓarɓarewa musamman a Arewa maso Yamma
FCT Abuja - Hukumar nan da gwamnatin tarayya ta kafa wacce zata maida hankali wajen daƙile yaɗuwar makamai (NATCOM) ta ce ta gama shirye-shiryen ɗaukar ma'aikata 300,000.
Rahoton jaridar Aminiya ya tattaro cewa hukumar zata ɗauki ma'aikata a kowane ɓangaren kasar nan kuma zata ba su horo na musamman domin dakile yawaitar yawon makamai.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da 'yan Najeriya ke fama da matsalar tsaro a sassa daban-daban kama daga barazanar hare-haren yan bindiga, yan ta'adda da sauransu.
Muƙaddashin shugaban NATCOM na ƙasa, Otunba Adejare Rewane, shi ne ya bayyana shirin ɗaukar ma'aikatan a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, 27 ga watan Agusta, 2023.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Adadin ma'aikatan da hukumar zata ɗauka a kowace jiha
Mista Rewane ya bayyana cewa hukumar NATCOM zata ɗauki adadin mutane 7,000 a kowace jiha daga cikin jihohi 36 na Najeriya da babban birnin tarayya Abuja.
A kalamansa, muƙaddashin shugaban NATCOM ya ce:
"Zamu ɗauki ma'aikata 300,000 a sassan Najeriya a kokarin ganin an samu tabbataccen zaman lafiya. Bayan ɗaukar aikin zamu ba su horo na musamman."
"Wannan mataki ka ɗaukar ma'aikatan zai rage yawan zaman kashe wando a ƙasa kuma zamu yi aiki kafaɗa da kafaɗa da sauran hukumomin tsaro domin cimma nasara."
"Duk mai son shiga wannan aiki ya riƙa bibiyar jaridu domin ganin matakan da za a bi amma zamu fi maida hankali kan matasa."
Shekara 2 Abiodun Yana Rike Kuɗin Kananan Hukumomi
A wani rahoton kun ji cewa Shugaban ƙaramar hukumar Ijebu ta gabas ya kai ƙorafin gwamnan Ogun ga tsohon gwamna, Aremo Olusegun Osoba.
Ciyaman ɗin ya zargi gwamna Abiodun da turmushe kason kuɗin kananan hukumomin da gwamnatin tarayya take turo wa duk wata na tsawon shekaru biyu da suka wuce.
Asali: Legit.ng