Kungiyar NURTW Ta Ce Ana Shirya Kai Ma Ta Hari a Babbar Sakatariyarta Ta Kasa

Kungiyar NURTW Ta Ce Ana Shirya Kai Ma Ta Hari a Babbar Sakatariyarta Ta Kasa

  • Kungiyar NURTW ta ce wasu mutane na shirin farmakar babbar sakatariyarsu da ke Abuja
  • Ƙungiyar ta ce mutanen na son fakewa da sunan zanga-zanga ne domin su cimma mummunar bukatarsa
  • NURTW ta shawarci al'umma da su kasance a ankare, sannan ta sanar da jami'an tsaro domin ɗaukar mataki

FCT, Abuja - Kungiyar direbobin motocin sufuri ta ƙasa (NURTW), ta nuna fargaba kan shirin da wasu mutane ke yi na gudanar da zanga-zanga a babbar sakatariyar kungiyar da ke Garki 2, Abuja.

Ƙungiyar ta ce wasu mutane ne ke son ɓoyewa da sunan zanga-zanga kan wani taro da ta gudanar domin tayarwa da mazauna birnin tarayya hankali kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

An bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa ta haɗin gwiwa tsakanin shugaban ƙungiyar na ƙasa, Alhaji Tajudeen Ibikunle Baruwa da sakatarenta, Anthony Asogwa Chukwudi ranar Litinin a Abuja.

Kara karanta wannan

To fah: Kasar Kamaru za ta sako ruwa da madatsa, za a yi ambaliya a Najeriya

NURTW ta ce wasu na yunkurin kai ma ta hari
Kungiyar NURTW ta ce ana yunƙurin farmakar babbar sakatariyarta da ke Abuja. Hoto: Abubakar S Rafi
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

NURTW ta samu bayanai kan shirin kawowa sakatariyarta hari

NURTW ta ce labari ya iso ma ta kan shirin da wasu ɓata gari suke yi na kutsawa cikin sakatariyar domin aikata ta'addanci.

Ana dai alaƙanta hakan da taron da masu zaɓe da masu ruwa da tsaki na kungiyar suka gudanar a Lafia babban birnin jihar Nasarawa a ranar Laraba, 23 ga watan Agusta.

Kungiyar ta NURTW ta bayyana zanga-zangar da aka shirya a matsayin wani gangami na nuna ƙin jinin shugabannin kungiyar da nufin haifar da rikici.

NURTW ta ankarar da jama'a gami da sanar da jami'an tsaro

Ƙungiyar ta NURTW ta kuma ƙara da cewa sun samu labari mai inganci cewa an ɗauko yan daba da aka shirya za su gudanar da mummunan aikin kuma an faɗa mu su abinda za su yi.

Kara karanta wannan

Rikicin Jamhuriyar Nijar: Jerin Manyan Abubuwa 5 Da Suka Faru Cikin Makon Nan

Ƙungiyar ta ce ta riga da ta sanar da jami'an tsaro dangane da halin da ake ciki a yanzu domin ɗaukar matakan da suka dace.

Haka nan kuma ƙungiyar ta NURTW na kira ga mazauna babban birnin na tarayya da su kasance masu lura da sanya idanu kan mutanen da ke son tayar da zaune tsaye.

Wannan dai ba shi ba ne karo na farko da ƙungiyar ta NURTW ke fitar da irin wannan sanarwa kan yunkurin kai ma ta farmaki kamar yadda Leadership ta wallafa.

Zulum ya samar da motoci 300 na kai manoma gonakinsu a Borno

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan matakin da gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya ɗauka na samar da motoci 300 domin jigilar manoman jihar zuwa gonakinsu.

Zulum ya ce ya ɗauki wannan mataki ne domin ragewa manoman jihar raɗaɗin da cire tallafin man fetur ya jefa su a ciki.

Kara karanta wannan

Sauki Ya Zo: Gwamnatin Tinubu Ta Faɗi Abun Alkairin da Zai Faru Kan Man Fetur a Karshen 2023

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng