Sabuwar Dirama Yayin Da DSS Suka Hana Mataimakin Gwamnan Edo, Shaibu Daga Ganin Gwamna Obaseki

Sabuwar Dirama Yayin Da DSS Suka Hana Mataimakin Gwamnan Edo, Shaibu Daga Ganin Gwamna Obaseki

  • Dangantaka na ƙara tsami tsakanin gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki da mataimakinsa Philip Shaibu
  • Hakan ya ƙara fitowa fili ne bayan jami'in tsaron na DSS ya hana mataimakin gwamnan ya gaisa da gwamnan a bainar jama'a
  • Obaseki wanda aka yi komai a gabansa bai ce uffan ba dangane da kunyata mataimakin gwamnan da aka yi

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Edo - Rikicin da ke tsakanin gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki da mataimakinsa, Philip Shaibu, ya sake ɗaukar sabon salo lokacin da jami'an hukumar DSS suka hana Shaibu ganin gwamnan.

Shaibu yana ɗaya daga cikin baƙin da suka halarci addu'o'in da aka gudanar a coci domin murnar cikar shekara 32 da ƙirƙiro jihar Edo, rahoton Daily Trust ya tabbatar.

Jami'an DSS sun hana Shaibu ganin Obaseki
Jami'an DSS sun hana Shaibu ganin Obaseki a coci Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

A wajen yin addu'o'in wanda aka gudanar a ɗakin taro na Festival Hall a gidan gwamnatin jihar a birnin Benin ranar Lahadi, Shaibu ya je wurin gwamnan domin ya gaida shi, amma sai jami'in DSS ya hana shi.

Kara karanta wannan

Shugaban 'Yan Bindiga Ya Ayyana Kansa a Matsayin Gwamnan Jihar Arewa? Gaskiya Ta Bayyana

Obaseki, wanda yake zaune tare da matarsa, Betsy da Charles Aniagwu, kwamishina daga jihar Delta, sai ya kawar da kansa yayin da Shaibu yake ƙoƙarin yi wa jami'an bayani wanda ya ƙi yarda ya bar shi ya ga gwamnan.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Bayan duk ƙoƙarin da mataimakin gwamnan ya yi domin ganin ya ga gwamnan ya ci tura, sai ya haƙura ya koma wajen zamansa, cewar rahoton The Punch.

Aikinsa kawai jam'in DSS yake yi

Da yake magana a kan lamarin, kakakin watsa labaran gwamnan, Andrew Okungbowa, ya bayyana cewa jami'in DSS ɗin aikinsa kawai yake yi.

A kalamansa:

"Duk abinda ya faru a wajen ba gwamna ba ne ya sanya kuma baya da masaniya kan abin da jami'an tsaron ke yi. A taƙaice jami'an tsaron aikinsu kawai su ke yi. Bayan haka gwamnan bai san cewa mataimakinsa ya zo domin gaida shi ba."

Kara karanta wannan

Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un, An Tsinci Gawar Shugabar Alkalai a Yanayi Mara Kyau a Jihar Arewa

"Coci waje ne da ake tara mutane, saboda haka jami'an tsaro suna da haƙƙin kare gwamna a wajen."

Shaibu ya yi martani

Duk da kunyata shi da aka yi, Shaibu ya ƙara tabbatar da cewa har yanzu yana tare da gwamnan kuma a shirye yake ya yi masa biyayya.

Da yake magana da manema labarai a wajen, mataimakin gwamnan ya bayyana Obaseki a matsayin babban yayansa.

Shaibu, wanda ya fito daga yankin Edo ta Arewa, yana son ya gaji Obasaki wanda ya fito daga yankin Edo ta Kudu, amma gwamnan yana son magajinsa ya fito daga yankin Esanland na Edo ta Tsakiya.

Hannatu Musawa Ba Ta Yi Laifi Ba

A wani labarin kuma, wani lauyan kundin tsarin mulki ya goyi bayan Hannatu Musawa kan dambarwar da ake yi a kanta kan rashin kammala NYSC.

Barr. Festus Ogun ya bayyana cewa ministar ba ta buƙatar satifiket ɗin NYSC domin samun muƙamin minista.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng