Hannatu Musawa Ta Karyata Rade-Radin Cewa Ta Yi Martani Kan Saba Dokar NYSC Da Ake Yadawa

Hannatu Musawa Ta Karyata Rade-Radin Cewa Ta Yi Martani Kan Saba Dokar NYSC Da Ake Yadawa

  • Yayin da ake ta cece-kuce kan batun bautar kasa na ministar al'adu, Hannatu Musawa, ta fito ta yi bayani
  • An yi ta yada jita-jita cewa ministar ta yi martani game da cece-kucen da ake yi kan NYSC da ta ke yi yanzu
  • Sai dai Barista Musawa ta karyata hakan inda ta ce ita ba ta yi wani martani game da hakan ba

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja – Ministar Al’adu, Hannatu Musawa ta karyata cewa ta yi martni kan cece-kucen da ake yi na bautar kasa da kuma kasancewarta minista da a ke yi.

A kwanakin nan ana ta cece-kuce kan batun bautar kasa na ministar inda wasu ke ganin ta sabawa doka ganin cewa a yanzu ta ke gudanar da bautar kasarta.

Musawa ta karyata cewa ta yi martani game da NYSC
Hannatu Musawa Ta Yi Sabon Martani Game Da Cece-kuce Na NYSC. Hoto: @HanneyMusawa.
Asali: Twitter

Me ya jawo martanin Musawa kan NYSC?

Kara karanta wannan

Hannatu Musawa: Shin Masu Yi Wa Kasa Hidima Na Iya Zama Minista? Falana, Sauran Lauyoyi Sunyi Martani

Wannan na zuwa ne bayan nadin Hannatu Musawa a matsayin minista tare da sauran wadanda aka rantsar a fadar Shugaba Tinubu, PM News ta tattaro.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Hukumar Matasa Masu Yi Wa Kasa Hidima (NYSC) ta yi martani game da hakan inda ta ce ministar ta ki zuwa bautar kasan a shekarar 2013.

Yayin da mutane da dama su ke korafin cewa ba ta dace da mukamin minista ba dai-dai lokacin da ta ke bautar kasa.

Har ila yau, a jiya Lahadi 27 ga watan Agusta, an ruwaito Hannatu Musawa ta na martani game da lamarin inda ta ce babu wata doka da ta karya na kasancewarta minista da kuma ‘yar bautar kasa.

Amma a wata sanarwa da mataimakin daraktan yada labarai na ma’aikatar yada labarai da wayar da kan jama’a, Suleiman Haruna ya ce martanin bai fito daga ministar ba.

Kara karanta wannan

“Na Tuba Daga Yanzu”: Budurwa Ta Kona Dukka Kayanta Da Ke Nuna Tsaraici, Ta Zama Kirista Ta Gaske

Ta ce babu wani martani da ta yi kan wannan lamari na NYSC kamar yadda ake yadawa a kafafen sadarwa.

Meye Musawa ta ce kan martanin NYSC?

Cewar sanarwar:

“Ministar al’adu, Barista Hannatu Musawa ta kadu da ganin bayanan da ake yadawa cewa ta yi martani game da NYSC, ta ce wannan labari ba daga gare ta ya ke ba.
Ministar ta tabbatar cewa ba ta fitar da wata sanarwa game da wannan cece-kuce ba inda ta bukaci mutane su yi taka tsan-tsan da irin wadannan bayanai.
“Don tabbatarwa, ina amfani da wannan dama wurin bayyanawa mutane cewa babu wata sanarwa da na fitar a kan wannan lamari.”

NYSC: Babu Dokar Da Ta Haramtamin Zama Minista, Musawa

A wani labarin, Ministar Al'adu a Najeriya, Hannatu Musawa ta yi martani game da cece-kucen da ake yi na bautar kasarta.

Musawa kamar yadda rahotanni su ka tabbatar ta ce babu inda ta karya doka na kasancewarta minista kuma mai bautar kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.