Ku Dena Zagin Ma'aikatan Lantarki, Minista Ya Roki Yan Najeriya

Ku Dena Zagin Ma'aikatan Lantarki, Minista Ya Roki Yan Najeriya

  • Ministan wutan lantarki ya roki yan Najeriya su dinga karfafa gwiwar ma'aikatan lantarkin maimakon zagi
  • Mr Adebayo Adelabu ya bayyana haka ranar Juma'a yayin wata ziyara a garin Oyo da ke Jihar Ibadan
  • Ministan ya kuma ce ma'aikatar karkashin jagorancinsa za ta fitar da sabbin hanyoyi da za su bunkasa samar da wutar lantarki a fadin Najeriya

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Oyo, Jihar Ibadan - Ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu, ya roki yan Najeriya da su daina zagin ma'aikantan lantarki.

Maimakon haka, ministan ya bukaci da su dinga karfafa musu gwiwa da goya musu baya.

Ministan Lantarki ya roki yan Najeriya su dena zagin ma'aikatan lantarki
An roki yan Najeriya su dena zagin ma'aikatan lantarki. Hoto: Photo Credit:@BayoAdelabu
Asali: Twitter

Ya yi rokon ne a ranar Juma'a yayin ziyarar da ya kai ga yan asalin Ibadan a Ibadan, babban birnin Jihar Oyo kamar yadda The Punch ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Ibrahim Geidam: Muhimman abubuwa 6 da baku sani ba game da ministan harkokin 'yan sanda

Za mu aiwatar da dokar lantarki ta 2023, Adelabu

Adelabu ya ce shirinsa shine aiwatar da dokar wutar lantarki ta 2023 wanda ta zo da sabbin hanyoyin samar da wutar lantarki da kuma yadda za a hada kai tsakanin gwamnatin tarayya da na jihohi.

Ministan ya ce ma'aikatar a karkashin jagorancinsa zata kara kyautata alaka tsakanin bangarori masu zaman kansu da na gwamnati don dorawa akan inda magabatansa suka tsaya.

Ya ce:

"Dokar wutar lantarki ta 2023 ta kara samar da wadatar wuta a Najeriya. Saboda haka, zan yi kokarin ganin kowanne gwamna ya gabatar da kudirin lantarki a jiharsa.
"Bayan haka, ina so nayi alkawarin cewa dam din Ikere Gorge zai samar da 20 KVA na lantarki. Ikere Gorge Dam na daya daga cikin manyan dam da Ogun - Osun River Basin Development Authority ta samar don samar da ruwa daga kofin Ogun."

A nasa bangaren, shugaban kungiyar CCII, Niyi Ajewole, ya shawarci ministan da ya hada kai da Gwamma Seyi Makinde don cigaban Ibadan dama jihar baki daya.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tarayya Ta Ba Tsohon Shugaban EFCC Bawa Damar Ganin Lauyoyi Da Yan Uwansa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164