Dan Shugaban Jam'iyyar APC Na Jihar Sokoto Ya Rasu a Wani Mummunan Hatsari

Dan Shugaban Jam'iyyar APC Na Jihar Sokoto Ya Rasu a Wani Mummunan Hatsari

  • Anas Isa Sadiq Acida, ɗan shugaban jam'iyyar APC a jihar Sokoto, Isa Sadiq Acida, ya rasu a wani mummunan hatsarin mota a safiyar ranar Asabar
  • Anas ya rasu tare da abokinsa, Umar Muhammad, mai shekara 22 a duniya wanda yake 300L a jami'ar Lead City a Ibadan
  • Mamacin yana kan hanyarsa ta dawowa gida ne daga jami'ar bayan ya kammala karatunsa na digiri

Jihar Sokoto - Shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na jihar Sokoto, Isa Sadiq Acida, ya shiga cikin jimami a safiyar ranar Asabar, 26 ga watan Agusta.

Shugaban jam'iyyar ya rasa ɗansa, Anas Isa Sadiq Acida, a wani mummunan hatsarin mota.

Dan shugaban APC na Sokoto ya rasu
Dan shugaban APC na Sokoto ya rasu a hatsarin mota Hoto: APC Sokoto
Asali: Twitter

A cewar rahoton jaridar Tribune, Anas mai shekara 25 a duniya wanda ya karanci Injiniya a jami'ar Lead City a birnin Ibadan, ya rasu ne a kan hanyarsa ta zuwa Sokoto bayan ya kammala karatunsa.

Kara karanta wannan

Atiku vs Tinubu: Jigon APC Ya Yi Hasashen Hukuncin Da Kotu Za Ta Yanke

Dan shugaban jam'iyyar APC da abokinsa sun rasu a hatsarin mota

Anas ya rasu ne tare da abokinsa Umar Muhammad mai shekara 22 wanda ya ke a 300L a jami'ar Lead City a Ibadan.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Abokanan junan su biyu sun rasu ne a safiyar ranar Asabar a wani mummunan hatsarin mota da ya auku a kan hanyar Yauri, a jihar Sokoto.

Ahmed Aliyu, gwamnan jihar Sokoto ya halarci jana'izar marigayi Anas Isa Saddiq Achida sannan ya yi ta'aziyya ga mahaifinsa da ƴan uwansa inda ya ƙara da cewa rasuwarsa babban rashi ne ga jihar.

Gwamna Aliyu ya yi ta'aziyya ga shugaban APC

Aliyu ya bayyana cewa marigayi Anas mutumin kirki ne mai ƙanƙan da kai da hazaƙa. Ya yi addu'ar Allah ya karɓi ayyukan alkhairin da ya yi sannan ya yafe masa kurakuransa.

Kara karanta wannan

Za a yi ta: Faransa ta daga yatsa ga sojin Nijar bayan umarnin korar jakadanta a kasar

Gwamnan ya buƙaci mahaifansa da su ɗauki rasuwar a matsayin muƙaddari daga Allah, sannan ya yi addu'ar Allah ya yi masa rahama.

Kotu Ta Tanaɗi Hukunci Kan Shari'ar Gwamnan Sokoto

A wani labarin ma daban kuma, kotun sauraron ƙarar gwamnam jihar Sokoto ta tanadi hukuncinta kan ƙarar da ke neman a ƙwace nasarar gwamna Ahmed Aliyu.

Kotun ta bayyana cewa za ta sanar da ɓangarorin biƴu ranar da za ta bayyana hukuncinta a cikin watan Satumba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng