Shugaba Tinubu Ya Turawa Jihar Ogun Buhunan Shinkafa 3,000 a Matsayin Rage Radadin Cire Tallafin Man Fetur
- Tuni gwamnatin jihar Ogun ta fara tsara yadda da ta yi rabon kayayyakin abinci ga marasa galibi
- Gwamnatin Tarayya ta umarci a ba jihohi kudade domin siya wa talakawa kayan abinci a shekarar nan
- Tun bayan cire tallafin man fetur ake fama da matsanancin fatara a Najeriya saboda haihuwar farashin kayayyaki
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Ogun - Gwamnatin jihar Ogun ta karbi buhunan shinkafa guda 3,000 na farko daga gwamnatin tarayya domin cika alkadarin shirinta na raba abinci ga ‘yan Najeriya domin rage tasirin cire tallafin man fetur, The Nation ta ruwaito.
Sakataren gwamnatin jihar Ogun, Mista Olatokunbo Talabi, wanda ya tabbatar da hakan a ranar Juma’a yayin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai, ya ce za a fara rabon shinkafar ne bayan an kammala shirin rabon.
Talabi ya kuma tabbatar da cewa gwamnatin jihar ta karbo kudi daga gwamnatin tarayya domin siyan hatsi a wani bangare na kudin da aka tsara na siyan kayayyakin abinci da kowace jiha za ta rabawa mazaunanta.
Gwamnatin jihar Ogun za ta yi karin tallafi
Sakataren ya yi nuni da cewa, gwamnatin jihar na kara sayo hatsi don karawa kan wanda gwamnatin tarayya ta bayar domin isar mazauna jihar, rahoton Daily Post.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A cewarsa, za a fara mai da hankali ga marasa galihu da kuma nasassu da mata a wannan rabon kayayyakin abinci da za a yi nan kusa.
Ya ce:
“Za a ba da kulawa ta musamman ga tsofaffi, nakasassu, da mata, da sauransu, wajen rabon kayayyakin.”
Ya kara da cewa tuni gwamnatin jihar ta kafa kwamitin mutane masu kishin da za su ruwa su yi tsaki wajen tabbatar da rabon kayan tallafin.
Akwai yiwuwar a dawo da tallafin man fetur
A wani labarin, Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya na tunanin fito da wani tsarin wucin gadi na tallafin man fetur lura da halin da ake ciki.
A sakamakon yadda farashin gangar mai da kudin kasar waje su ka tashi, The Cable ta ce Mai girma Bola Ahmed Tinubu zai iya lashe amansa.
Fadar shugaban kasa ba ta yanke matsaya ba tukuna, amma an bijiro da wannan magana kuma watakila shugaban kasar ya amshi shawarar.
Asali: Legit.ng