Kwamishinan Anambra Ya Bai Wa Yar Sanda Kyautar N250,000 Kan Kin Karban Cin Hanci
- Kwamishinan 'yan sanda ya bai wa jami'ar 'yan sanda mace kyautar N250,000 bisa nuna gaskiya da rikon amana a bakin aiki
- Insufekta Charity Oyor ta samu wannan kyauta sakamakon ƙin karban cin hanci daga wanda ake zargi a jihar Anambra
- Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar ya bayyana abinda ya faru har aka ba 'yar sandar cin hanci amma taƙi karɓa
Anambra state - Kwamishinan ‘yan sandan jihar Anambra, Aderemi Adeoye, ya baiwa wata ‘yar sanda, Insufekta Charity Oyor kyautar naira 250,000 bisa ƙin karbar cin hanci daga hannun wanda ake zargi.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ‘yan sanda reshen jihar Anambra, Tochukwu Ikenga, ya fitar ranar Juma’a, 25 ga watan Agusta.
Kakakin 'yan sandan ya bayyana cewa Insufekta Charity tana aiki ne a Caji Ofis ɗin babbar kasuwa da ke Onitsha, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.
Yadda yar sanda ta nuna gaskiya a bakin aiki
A cewarsa, 'yar sandan ta ki amincewa da cin hanci daga wani wanda ake zargin da ta kama yana dauke da manyan dami guda shida na wayar kebul da ake zargin an sace.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Kakakin 'yan sandan ya ce:
"Ta dakatar da direban sannan ta nemi asalin mai kayan, wanda maimakon ya yi mata bayanin yadda ya mallaki wayar sai ya ba ta cin hanci amma ta ƙi karba."
“Nan take jami'ar ta kira DPO, Insufekta Joy Chidinma Ikpeama wacce ta jagoranci jami’an ‘yan sanda zuwa wurin kuma ta kama wanda ake zargin. An kama kayan ana bincike."
“A caji ofis ɗin, wanda ake zargin ya sake bayar da cin hancin N500,000 don a bar shi ya tafi, jami’ai suka ƙi karba. Nan take DPO ta yi wa kwamishinan ‘yan sandan bayanin abinda ya faru."
Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un, An Tsinci Gawar Shugabar Alkalai a Yanayi Mara Kyau a Jihar Arewa
Daga nan ne aka maida Kes din lamarin zuwa sashin binciken muggan laifuka (CID) na rundunar yan sandan jihar da ke Awka, in ju rahoton Premium Times.
A wajen gabatar da kyautar tsabar kuɗin ga yar sandan ranar Jumu'a, Kwamishinan ya yabawa Insufekta Charity bisa riƙo da gaskiya.
Ana Fargabar Soja Ya Mutu Yayin da Yan Bindiga Suka Farmaki Motar Sojoji
A wani rahoton Wasu 'yan bindiga sun yi wa motar sojojin Najeriya kwantan ɓauna, sun halaka soja ɗaya a babban birnin jihar Edo.
'Yan bindiga sun farmaki motar sintirin jami'an sojin ba zato ba tsammani, inda suka yi ajalin soja guda ɗaya a jihar Edo.
Asali: Legit.ng