Dalibin Ajin Karshe Na Jami'ar FUTA Ya Fadi Kasa Matacce Yayin Da Yake Shirin Zana Jarabawar Karshe

Dalibin Ajin Karshe Na Jami'ar FUTA Ya Fadi Kasa Matacce Yayin Da Yake Shirin Zana Jarabawar Karshe

  • Ɗaliban jami'ar Fasaha ta jihar Ondo da ke Akure, sun gudanar da zanga-zanga a bakin makarantar
  • Zanga-zangar ta biyo bayan mutuwar wani ɗalibin jami'ar da ke shirin rubuta jarabawarsa ta ƙarshe
  • Ɗaliban sun alaƙanta mutuwar ɗalibin da sakacin ma'aikatan lafiyar asibitin jami'ar

Akure, jihar Ondo - An shiga ruɗani yayin da wani ɗalibin ajin ƙarshe na jami'ar Fasaha ta Akure (FUTA), da ke jihar Ondo ya fadi ƙasa matacce.

Harkokin makarantar duka sun tsaya cak, biyo bayan zanga-zangar da wasu daga cikin ɗaliban makarantar suka gudanar bayan faruwar lamarin in ji Daily Trust.

Dalibin ajin ƙarshe na jami'ar FUTA ya rasa ransa
Dalibin anin karshe ya fadi ƙasa matacce yana shirin rubuta jarabawar karshe. Hoto: Federal University of Technology Akure
Asali: Facebook

Yadda ɗalibin ajin ƙarshe ya faɗi ƙasa matacce

An bayyana cewa Ayomide Akeredolu, ɗalibin aji biyar na jami'ar FUTA, ya faɗi ƙasa ne a cikin ɗakin kwanan ɗaliban makarantar a yayin da ake ta shirye-shiryen rubuta jarabawa.

Kara karanta wannan

Yanzu: Nijar Ta Kulla Kawance Na Soji Da Kasashe 2 Masu Karfin Fada a Ji Gabanin Yaƙi Da ECOWAS

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Faduwarsa ke da wuya sai jama'ar da ke wurin suka yi ƙoƙarin garzayawa da shi ɗan ƙaramin asibitin da ke cikin makarantar, inda a can ne ya ce ga garinku nan.

Jin labarin mutuwar ta sa ya harzuƙa wasu daga cikin ɗaliban makarantar, wanda hakan ya kai ga gudanar da zanga-zanga a kan titin da ke gaban makarantar na tsawon sa'o'i masu yawa.

Ɗaliban sun yi zargin cewa sakacin ma'aikatan asibitin makarantar ne ya janyo mutuwar ɗalibin.

Ɗalibin ya riga da ya mutu lokacin da aka kawo shi, jawabin asibitin

Sai dai hukumar makarantar a yayin da take miƙa saƙon ta'aziyyarta ga iyaye da 'yan uwan mamacin, ta ce lokacin da aka kawo shi asibitin ya riga da ya mutu.

Mai magana da yawun hukumar makarantar, Adegbenro Adebanjo ya ce yana da kyau jama'a su fahimci cewa zanga-zangar ba ta da alaƙa ya kai tsaye da mutuwar ɗalibin.

Kara karanta wannan

'Yan Ta'adda Sun Shiga Uku, Hukumar NAF Ta Bayyana Wani Muhimmin Shiri Da Take Musu

Ya ƙara da cewa likitocin da ke kan aiki sun yi iya bakin ƙoƙarinsu wajen ceton rayuwarsa, amma hakan bai yiwu ba tunda a mace aka kawo shi.

Lamarin dai ya faru ne a ranar Alhamis, 24 ga watan Agusta kamar yadda jaridar The Punch ta wallafa.

Abba ya ware miliyan 700 don biyawa dalibai kuɗin makaranta

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan zunzurutun kuɗi har naira miliyan 700 da gwamnan jihar Kano, Abba Gida Gida ya ware don biyawa ɗaliban jihar kuɗin makaranta.

Hakan dai na cikin ƙudurin gwamnatin na ganin ta taimakawa 'ya'yan marasa galihu a harkokin karatunsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng