Shugaba Tinubu Ya Bayyana Aniyar Gwamnatinsa Na Kawo Karshen Cin Hanci A Bangaren Shari'a
- Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya bayyana aniyarsa ta kawo karshen cin hanci a bangaren shari'ar kasar
- Tinubu ya bayyana haka ne yayin karbar bakwancin shugaban Kungiyar Lauyoyi ta Kasa, NBA, Barista Yakubu Maikyau a Abuja
- Shugaban ya ce gwamnatinsa ta himmatu wurin dakile cin hanci amma hakan zai yi wahala har sai an gyara albashin alkalai
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
FCT, Abuja - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi alkawarin kawo sauyi a albashin alkalai don dakile cin hanci.
Tinubu ya bayyana haka ne yayin karbar bakwancin shugaban Kungiyar Lauyoyi ta Najeriya (NBA), Barista Yakubu Maikyau.
Meye Tinubu ya ce game da alkalai?
Tinubu ya ce gwamninsa ta himmatu wurin gyara albashin alkalai don rage cin hanci a tsakaninsu, Tribune ta tattaro.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin wata sanarwa, hadimin shugaban, Ajuri Ngelale ya ce yaki da cin hanci ba zai yiyu ba sai idan an gyara albashi da alawus na alkalai.
Ya ce wannan shi ne muhimmin abu da ya kawo ci gaba a harkokin shari'a lokacin mulkinsa a jihar Legas.
Sanarwar ta ce:
"Dole mu gyara albashin alkalai da alawus na su idan mu na son kawo karshen cin hanci da rashawa.
"Za mu yi duba ga yawan kudaden da kuma matsalolin da ke ciki."
Tinubu ya godewa lauyoyin bisa ziyarar
Shugaba Tinubu ya godewa kungiyar lauyoyin bisa ga karrama shi tare da gayyatar shi zuwa babban taron su a Abuja a wannan sati.
Tinubu ya bayyana jin dadinsa ganin yadda ya samu daman aiki da lauyoyi a matsayin hadimai, cewar The Guardian.
Daga cikin lauyoyin akwai shugaban ma'aikata, Femi Gbajabiamila da mai kula da tsare-tsare, Ambasada Victor Adeleke.
Tinubu Ya Bayyana Matsayarsa Kan Tallafin Kudade Na Jihohi
A wani labarin, Shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa ba zai iya tilasta gwamnoni kan yadda za su raba kudaden tallafi na Naira biliyan biyar ba.
Tinubu ya bayyana haka ne yayin da malaman addinin Musulunci su ka roke shi da ya shiga lamarin don yin adalci a rabon kudin.
Ya ce a tsarin dimukradiyya sai dai ya roke su don aiwatarwa amma ba zai zauna daga nan ya na umurtansu ba.
Asali: Legit.ng