Jam'iyyar PRP Ta Gargadi Shugaba Tinubu Kan Yaki Da Nijar
- Tsoma bakin da Najeriya ke yi a kan rikicin juyin mulkin Jamhuriyar Nijar bai yi wa jam'iyyar Peoples Redemption Party (PRP) daɗi ba
- Mai bada shawara a kan shari'a na ƙasa na jam'iyyar ya fito ya caccaki yadda Najeriya ta yi ruwa ta yi tsaki dangane da rikicin na Nijar
- Farfesa Aliyu Mahmood ya yi nuni da cewa kamata ya yi ƙasar nan ta mayar da hankali wajen magance tarin matsalolin da take fuskanta ba wai afkawa maƙwabciyarta da yaƙi ba
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Kwara - Jam'iyyar Peoples Redemption Party (PRP) ta soki tsoma bakin da Najeriya take yi wajen amfani da ƙarfin soja kan rikicin juyin mulkin Jamhuriyar Nijar.
Mai bada shawara a kan shari'a na jam'iyyar PRP, Farfesa Mahmood Aliyu, shi ne ya yi sukar yayin zantawa da manema labarai a birnin Ilorin, babban birnin jihar Kwara a ranar Juma'a, cewar rahoton Leadership

Source: Twitter
Mahmood ya yi nuni da cewa Najeriya tana da tarin matsaloli da suka dabaibayeta waɗanda ke buƙatar a magancesu, ba wai ɓata kuɗin ƙasa ba wajen kai hari a Nijar.
Sai dai, ya yi maraba da shiga tsakanin da ECOWAS ke yi domin magance rikicin na Nijar, inda ya ƙara da cewa hakan ba shi ba ne abinda Najeriya a ƙashin kanta yakamata ta ba muhimmanci ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yaki da Nijar ba matsalar Najeriya ba ce, Aliyu
A kalamansa:
"Ba mu magance matsalolin tsaronmu ba yadda yakamata. Wace hikima ce mu ke da ita da za mu farmaki maƙwabciyarmu da yaƙi? Maganar gaskiga har cikin zuciyata ina adawa da hakan. Kwata-kwata hakan bai dace ba ta kowace irin fuska."
"Wannan rikicin bai kamata ya zama abin da yakamata mu ba muhimmanci ba ne a ƙasar nan. Amma idan a matakin ECOWAS ne hakan ya yi daidai. Lamarin ma ya ɗauki fuskar siyasa da ƙabilanci."
Tinubu Ya Hana ECOWAS Aukawa Nijar
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa da ba domin shi ba da tuni ECOWAS ta aukawa Jamhuriyar da yaƙi.
Shugaba Tinubu ya yi nuni da cewa shi ne ya dakatar da dakarun na ECOWAS shiga Nijar domin dawo da mulkin da sojoji suka ƙwace.
Asali: Legit.ng

