“Tana Biyan 238k Duk Wata”: Yar Najeriya Ta Baje Kolin Dakinta a Kasar Japan, Bidiyon Ya Yadu

“Tana Biyan 238k Duk Wata”: Yar Najeriya Ta Baje Kolin Dakinta a Kasar Japan, Bidiyon Ya Yadu

  • Wata matashiya yar Najeriya ta garzaya soshiyal midiya don nunawa duniya yadda fasalin dakinta yake a kasar Japan
  • A cewarta, tana biyan $309 (kimanin N238k duk wata) kuma ya zo da wasu kayan amfani a cikinsa
  • Masu amfani da Intanet da suka kalli bidiyon dakin nata sun yi martani kan gado, bandaki da sauran yankunan dakin nata

Wata matashiya yar Najeriya, Prospee, ta baje kolin dakinta na kasar Japan, wanda take biyan $309 (kimanin N238k) duk wata a matsayin kudin haya.

Baya ga intanet mara yankewa, ta bayyana cewa dakin nata ya zo da gado, talbijin, na'urar dumama abinci, firinji, na'urar sanyaya wuri da injin wanki.

Dakin da wata yar Najeriya ke haya a kasar Japan
“Tana Biyan 238k Duk Wata”: Yar Najeriya Ta Baje Kolin Dakinta a Kasar Japan, Bidiyon Ya Yadu Hoto: @pros_peee
Asali: TikTok

An fara zagaya dakin Prospee ne daga kofar shiga sannan aka shiga bandakinta wanda take ganin ya yi kankanta.

Kara karanta wannan

Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un, An Tsinci Gawar Shugabar Alkalai a Yanayi Mara Kyau a Jihar Arewa

Wani abun burgewa game da dakin shine cewa fitilan dakin na da rimot. Wato kenan ana iya kunnawa da kashewa daga koina maimakon daga jikin bango.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"...Zagayen dakina na Japan.
"Hayan gida a Japan ya kai kimanin 30-50k yen ya danganta da inda kake zama da kuma irin dakin da kake zaune.
"Dakina ya zo da kayan daki (Firinji, Talbijin, injin wanki, na'urar dumama abinci, na'urar sanyaya wuri da gado). da kuma intanet mara yankewa," ta rubuta a TikTok.

Mutane sun yi martani a kan bidiyon Prospee

amytexamarachi ta ce:

"Wato kin dauki ruwan goran eva zuwa China."

fazza45 ya ce:

"Ya fi na Dubai kyau sosai."

OMOKAYODE ya ce:

"Yaya kike fama da banbancin yare."

bonitawilliams469 ta ce:

"Yanzu kowa na son zuwa Japan harda wadanda basu da fasfot.

L Y O N ta ce:

Kara karanta wannan

“Buhun Shinkafa N350”: Budurwa Ta Baje Kolin Kayayyakin Da Mahaifinta Ya Yi a 1990, Farashin Kayayyakin Ya Ba Da Mamaki

"Najeriya kuna yawo babu inda babu ku a duniyar nan."

Almira ta ce:

"Yar uwa ina shirin komawa chan fa ban san wa zai sani a hanya ba shin makaranta kike yi a chan."

Sky ta ce:

"Ya yi arha amma dai gadon ya yi mun kankanta da yawa."

Yadda mai masara ta karkarya masara don saukakawa kwastamominta

A wani labarin, mun ji cewa wani hoto da ke yawo a Facebook ya nuno wata mai siyar da masara da ta yanka shi zuwa kanana-kana.

An gano matar zaune a bakin hanya, inda ta mayar a matsayin shagonta na siyar da gasasshen masara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng