Badaru, Matawalle Sun Samu Halartar Binne Gawarwakin Sojoji Da Su Ka Mutu A Neja
- A makon daya gabata, rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da kisan sojojinta 36 da 'yan bindiga su ka yi a jihar Neja
- Rundunar ta ce hakan ya biyo bayan kwanton bauna da 'yan bindigan su ka yi wa sojojin da kuma kado jirgin saman rundunar
- A yanzu haka ana bikin binne sojojin a jihar Neja inda ministan tsaro da mataimakinsa su ka samu halarta
Jihar Neja - A yanzu ana bikin binne gawarwakin sojoji akalla 20 da 'yan bindiga su ka yi ajalinsu a jihar Neja.
Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da mutuwar sojojinta 36 a makon daya gabata.
Yaushe aka kashe sojojin?
Wannan na zuwa ne yayin da 'yan bindiga su ka musu kwanton bauna a hanyar Zungeru zuwa Tegina da kuma kado jirgin sojin da 'yan bindiga su ka yi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daily Trust ta tattaro cewa yanzu haka ana kan binne sojojin inda ministan tsaro, Badaru Abubakar ya samu halarta.
Sauran wadanda su ka halarta akwai karamin ministan tsaro, Bello Matawalle da hafsan rundunar tsaro, Janar Christopher Musa, cewar PM News.
Jerin sunayen sojojin da ake binnewa a yau.
1. Marigayi Manjo SA ONI
2. Marigayi Laftanar ANTHONY DURYUMSU
3. Marigayi Laftanar IBRAHIM ADAMU
4. Marigayi Laftanar GM ODUSAMI
5. Marigayi Laftanar US ALKALI
6. Marigayi Sajen FARUK MOHAMMED
7. Marigayi IBRAHIM GARBA
8. Marigayi CHIROMA POGU
9. Marigayi ADAMA ISAAC
10. Marigayi HARUNA JAMILU
11. Marigayi SAMAILA BASHIRU
12. Marigayi AB SULEIMAN MK (sojan ruwa)
13. Marigayi JAURO AMOS (sojan sama)
14. Marigayi SUNDAY OKOPI
15. Marigayi EKPANYO EDETD
16. Marigayi ALARIBE DANIEL (sojan sama)
17. Marigayi BRIGSS STEPHEN (sojan sama)
Abba Gida-Gida Ya Saki Miliyan 854 Don Auren Zawarawa a Jihar Kano, Zai Kuma Aiwatar Da Wasu Muhimman Ayyuka 2
18. Marigayi YAKUBU AYUBA
19. Marigayi NURA MOHAMMED
20. Marigayi HABIB ALIYU
21. Marigayi TANKO WAJE
22. Marigayi ABUBAKAR ABDULRAHAMAN (sojan sama)
Sojoji Sun Bayyana Yawan Jami'ansu Da Aka A Neja
A wani labarin, rundunar tsaro a Najeriya ta bayyana cewa 'yan bindiga sun kashe akalla jami'ansu guda 36 a jihar Neja.
Rundunar ta bayyana haka ne a ranar 17 ga watan Agusta a Abuja.
Ta ce kisan sojin na zuwa ne bayan 'yan bindiga sun yi musu kwanton bauna da kuma wadanda su ka kado a jirgin sama.
Asali: Legit.ng