"Ba Zan Iya Tsoma Baki A Harkar Rabon Tallafi Biliyan 5 Na Jihohi Ba", Tinubu Ya Yi Martani
- Shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewar ba zai iya umurtan gwamnonin jihohi ba kan yadda za su raba kudin tallafi
- Shugaban ya bayyana haka ne a yau Alhamis 24 ga watan Agusta yayin ganawa da malaman addini
- Ya ce ba zai zauna daga nan ya na bai wa gwamnoni umarni ba sai dai ya roke su don yin abin da ya dace
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
FCT, Abuja - Shugaban kasa, Bola Tinubu ya ce ba zai tsoma baki ba a yadda gwamnonin jihohi za su raba tallafin Naira biliyan biyar da ya bayar.
A kwanakin baya ne Shugaba Tinubu ya ware kudin tallafi don ragewa jama'a halin kuncin da su ke ciki.
Meye Tinubu ya ce wa malaman?
Tinubu ya ware Naira biliyan biyar ga ko wace jiha da kuma tirelolin abinci don taimakon 'yan kasar, PM News ta tattaro.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Shugaban ya bayyana haka yayin da ya ke ganawa da malaman addinin Musulunci a yau Alhamis 24 ga watan Agusta.
Malaman sun roki shugaban da ya taimaka ya shiga harkar rabon tallafin don gudanar da shi yadda ya kamata.
Amma a martaninsa, Tinubu ya ce ba zai iya ba su umarni ba na yadda za su raba kayan ganin cewa sun fi kusa da al'umma.
Ya ce:
"Mutane su na rayuwa a jihohinsu ne, ko da na kafa kwamiti sai na bi ta wurin gwamnoni da kananan hukumomi.
"Za mu ci gaba da yi wa gwamnonin magana, 'yan Najeriya su su ka sani."
Meye Tinubu ya ce game da gwamnonin?
Tinubu ya ce a tsarin dimukradiyya ba zai yiyu ya zauna daga gefe ya na umartan gwamnoni kan tsarin da za su bi na rabon tallafin ba, NTA News ta tattaro.
"Babu hakan a tsarin dokar dimukradiyya, shugaba ya zauna daga nan ya na bai wa gwamnoni umarni, sai dai na roke su don aiwatarwa.
"Mutane na rayuwa ne a jihohinsu, idan gwamnoninsu ba su yi abin da ya dace ba, mutane za su yi watsi da su a zabe."
Tinubu Ya Sake Tura Malaman Musulunci Zuwa Nijar
A wani labarin, Shugaba Bola Tinubu ya roki malaman addinin Musulunci da su koma Nijar don neman sulhu.
Tinubu ya yi rokon ne a yau Alhamis 24 ga watan Agusta a Abuja yayin da rikicin ya ki ci ya ki cinyewa.
Asali: Legit.ng