Hatsarin Jirgin Ruwa Ya Lakume Rayukan Mutum 12 a Jihar Nassarawa
- Wani jirgin ruwa da ya ɗauko mutane 19 ya nutse a yankin ƙaramar hukumar Lafia da ke jihar Nasarawa
- Majalisar dokokin jihar ta tabbatar da cewa mutane 12 daga ciki sun rasa rayukansu yayin 7 suka tsira da rayuwarsu
- Shugaban majalisar ya jajantawa iyalai, yan uwa da sauran mazauna Nasarawa bisa wannan rashi kana ya jagoranci shiru na minti ɗaya
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Nasarawa State - Majalisar dokokin jihar Nasarawa ta aike da saƙon ta'aziyya ga al'ummar yankin ƙaramar hukumar Lafiya sakamakon rasuwar mutum 12 a haɗarin jirgi.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa mutanen sun rasa rayukansu ne yayin da jirgin ruwan da su ke ciki ya kife a Kogin Kungra Kamfani da ke Arikiya a ƙaramar hukumar Lafiya.
Shugaban majalisar dokokin jihar Nasarawa, Ibrahim Balarabe Abdullahi, shi ne ya bayyana haka a zaman gaggawan da majalisar ta gudanar ranar Alhamis a Lafiya, babbar birnin jihar.
Ya kuma ƙara jajantawa da ta'aziyya ga iyalan waɗanda hatsarin ya rutsa da su bisa wannan babban rashi da suka yi.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Shugaban majalisar ya ce:
“Babban abin takaici ne yadda muka rasa mutane 12 da suka hada da maza da mata a wani hatsarin jirgin ruwa a garin Arikiya da ke karamar hukumar Lafia."
“Mutane 19 ne ke cikin jirgin, 12 sun mutu sannan an yi nasarar ceto 7. A halin yanzu karamar hukumar Lafia da jiharmu na cikin alhini kan wannan abin bakin ciki da ya faru."
Majalisar ta kuma bukaci ‘yan uwa, iyalai, karamar hukumar Lafia da kuma gwamnatin jihar Nasarawa da su ɗauki wannan rashi a matsayin kaddara daga Allah.
Ya ƙara da cewa:
“A madadina, ‘yan majalisa da ma’aikata, muna jajantawa iyalan mamatan, karamar hukumar Lafia da kuma gwamnatin jihar bisa wannan rashi. Muna rokon Allah ya jikan su."
Abba Gida-Gida Ya Saki Miliyan 854 Don Auren Zawarawa a Jihar Kano, Zai Kuma Aiwatar Da Wasu Muhimman Ayyuka 2
Daga nan sai mambobin majalisar dokokin suka yi shiru na tsawon daƙiƙu 60 domin girmama waɗanda suka rasu a haɗarin jirgin ruwan, Leadership ta tattaro.
Kotun Daukaka Kara Ta Tsige Shugaban LP na ƙasa
A wani rahoton na daban mun kawo muku cewa Kotu ta tsige shugaban Labour Party na ƙasa, Julius Abure.
Bayan tunɓuke Mista Abure, Kotun ta kuma amince da Lamidi Apapa a matsayin halastacccen shugaban jam’iyyar LP ta kasa.
Asali: Legit.ng