Hannatu Musa Musawa: An Bankado Wani Sabon Laifin Ministar Tinubu

Hannatu Musa Musawa: An Bankado Wani Sabon Laifin Ministar Tinubu

  • An sake taso sabuwar ministar fasaha, al'adu da tattalin arziƙin fikira, Hannatu Musa Musawa, a gaba
  • Ana zarginta da saɓawa tanadin kundin tsarin mulki wanda hakan ya sanya zamanta minista ya saɓa doka
  • A cewar ƙungiyar HURIWA, Hannatu yanzu haka tana yin bautar ƙasar ta (NYSC) a birnin tarayya Abuja

FCT, Abuja - Ana zargin Hannatu Musa Musawa, ministar fasaha, al'adu da tattalin arziƙin fikira, da kasancewa mai yin bautar ƙasa (NYSC) ƙafin naɗin da Shugaba Tinubu ya yi mata.

Kamar yadda Arise TV online ta rahoto, ƙungiyar HURIWA ita ce ta yi zargin, inda ta nuna cewa naɗin da aka yi mata ya saɓa doka.

Ana zargin Hannatu Musa da rashin kammala NYSC
Shugaba Tinubu tare da Hannatu Musa Musawa Hoto: @HonhanneyMusawa
Asali: Twitter

Ƙungiyar ta yi zargin cewa ministar tana bautar ƙasa ne a jihar Ebonyi, amma ta tsallake ta daina domin zama minista wanda a doka ba ta cancanta ba.

Kara karanta wannan

Wata Sabuwa: Wata Kungiya Ta Bukaci Ministocin Tinubu Su Yi Murabus, Ta Bayyana Dalilanta

An tattaro cewa tun a shekarun baya aka tura ta yin bautar ƙasar amma sai ta fasa, sannan daga baya ta dawo ta nuna sha'awar tana son kammalawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An sake tura ta bautar ƙasar a shekarar 2023, inda aka kai ta wajen wasu lauyoyi a birnin tarayya Abuja domin yin aiki a wajen, kafin a naɗa ta muƙamin minista.

HURIWA ta yi mamakin yadda aka yi hukumar ƴan sandan farin kaya (DSS) ba ta gano cewa Hannatu, bautar ƙasa take yi kafin tantanceta a matsayin minista.

A ina Hannatu Musawa ta ke bautar ƙasa yanzu haka?

Ƙungiyar ta bayyana cewa:

"Sashe na 13 na dokar NYSC, ya gindaya cewa duk wani ɗan Najeriya da ya kammala karatun digiri ko HND mai ƙasa da shekara 30 wanda ya ƙi zuwa yin bautar ƙasa na shekara ɗaya, ya aikata laifi wanda ya cancanci hukuncin tarar N4,000 ko ɗaurin shekara biyu a gidan kaso, ko hukuncin tara da zaman gidan kaso."

Kara karanta wannan

Shin Jam'iyyun PDP, NNPP Da LP Na Shirin Dunkulewa Waje Daya? Peter Obi Ya Bayyana Gaskiya

Ƙungiyar ta tabbatar da cewa majiyoyi masu tushe sun tabbatar da cewa har yanzu ministar ƴar bautar ƙasa ce kuma ba ta kammala ba.

Bayanan ɓautar ƙasar ta sun nuna lambar NYSC ɗinta a matsayin FC/23A/505 sannan an tura ta ne zuwa kamfanin Onyilokwu Onyilowa a 'Paint house old Banex Plaza'

Ragowar Kujerar Minista 2 Ta Kawo Rigima

A wani labarin kuma, kujerar minista ɗaya da ta rage Shugaba Tinubu ya naɗa na neman haɗa rigima a jam'iyyar APC

Wasu matasan jam'iyyar dai sun yi ruwa da tsaki sai an ba Seyi Tinubu kujerar muƙamin ministan matasa, yayin da wasu kuma ke goyon bayan shugaban matasan jam'iyyaar na ƙasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng