Nijar: Shugaba Tinubu Ya Sa Labule da Manyan Malaman Musulunci a Aso Villa
- Bola Ahmed Tinubu na gana wa yanzu haka da wakilan Malumman addinin Musulunci a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja
- Wannan taro na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan tawagar Malamai sun gana da jagoran sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar
- Ana tsammanin sun koma wurin shugaban ƙasa ne domin faɗa masa sakamakon tattaunawarsu da Abdourahamane Tchiani
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
FCT Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu na gana wa yanzu haka da wakilan malaman addinin Musulunci karƙashin jagorancin Sheikh Dahiru Usman Bauchi a fadarsa da ke Abuja.
The Nation ta ce idan baku manta ba tawagar Malaman Addinin Musulunci sun buƙaci a basu dama su shiga tsakanin sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar da ECOWAS.
Haka zalika a wannan lokaci shugaban ƙasa ya bai wa Malaman dama domin warware matsalar ba tare da an ɗauki matakin soji ba.
Abdulsalami: Sojojin Nijar Sun Ce Ba Zai Yi Wu Su Mayarwa Bazoum Mulki Ba, Sun Fadi Abinda Suke So a Yi Mu Su
Bayan haka Malaman sun ziyarci Jamhuriyar Nijar kuma sun samu zama da shugaban sojojin da suka yi juyin mulki, Abdourahamane Tchiani, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Dalilin da ya sa Malamai suka koma wurin Tinubu
Shugaba Tinubu, wanda ke jagorantar ƙungiyar bunƙasa tattalin arzikin ƙasashen yammacin Afirka (ECOWAS), ya karɓi bakuncin wakilan Malaman Musulunci yau Alhamis a fadar shugaban ƙasa.
An tattaro cewa manyan Malumman Musulmai sun sake komawa wurin Tinubu ne domin yi masa bayani kan sakamakon ziyarar da suka kai Jamhuriyar Nijar.
Idan dai za a iya tunawa kungiyar ECOWAS ta dauki matakin nuna rashin amincewarta da kwace ikon da sojoji suka yi a Nijar ta hanyar kakaba wasu takunkumi da kuma wa'adi.
Bugu da ƙari, ƙungiyar ta kuma yi barazanar ɗaukar matakin soji idan tattaunawar sulhu ta ci tura.
"Akwai Babbar Matsala" Fitaccen Malami Ya Bayyana Hukuncin da Kotu Zata Yanke Kan Nasarar Tinubu a 2023
Sai dai matakin sojin ne Malumman Musulunci na arewacin Najeriya ba su yarda ECOWAS ta ɗauka ba domin a ganinsu yaƙin ba iya Nijar kaɗai zai shafa ba.
Shugaban Sojojin Wagner Ya Mutu a Hatsarin Jirgin Sama
A wani labarin kuma Shugaban sojin haya na Wagner, Yevgeny Prigozhin, ya mutu a wani mummunan hatsarin jirgin sama a Moscow na kasar Rasha.
Ma'aikatar sufurin jiragen sama ta ƙasar Rasha ta fara bincike kan hatsarin jirgin wada ya auku a yankin Tver ranar Laraba, 23 ga watan Agusta, 2023.
Asali: Legit.ng