Kano: Kotu Ta Tura Magidanci Gidan Yari Saboda Dukan Tsohuwar Matarsa

Kano: Kotu Ta Tura Magidanci Gidan Yari Saboda Dukan Tsohuwar Matarsa

  • Kotun shari'ar Musulunci ta aika wani magidanci gidan yari bisa laifin dukan tsohuwar matarsa
  • Kotun ta kuma tuhumi mutumin mai suna Suleiman Shuaibu da ɓata sunan matar da ya daka
  • Hakan ya biyo bayan ganin matar da mijin ya yi da wani saurayi duk da cewa yanzu ba sa a tare

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Kano - Wata kotun shari'ar Muslunci da ke zamanta a Kano ta aike da wani magidanci mai suna Suleiman Shuaibu kan laifin dukan tsohuwar matarsa da kiranta da 'karuwa'.

Kotu ta tuhumi Shuaibu mai shekaru 46 kan amfani da ƙarfi da kuma ɓata sunan wacce ta yi ƙararsa kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

Kotu ta tura magidanci gidan yari a Kano
Kotu ta tura magidanci gidan yari kan lakaɗawa tsohuwar matarsa duka a Kano. Hoto: The Guardian
Asali: UGC

Yadda magidanci ya lakadawa tsohuwar matarsa duka

Jami'i mai gabatar da ƙara Aliyu Abideen, ya shaidawa kotu cewa matar mai suna Adama Munka'il ta shigar da koke kan lamarin a ofishin 'yan sanda na Zango da ke cikin birnin Kano a ranar 21 ga watan Agusta.

Kara karanta wannan

"Badakalar Miliyan 40": Amal Umar Ta Bayyana Gaskiyar Abun da Ya Wakana Tsakaninta Da Tsohon Saurayinta

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Adama ta shaidawa jami'an 'yan sandan cewa a ranar 18 ga watan Agusta ne tsohon mijin na ta ya lakaɗa ma ta duka sannan ya kuma kira ta da karuwa saboda ganinta da wani sabon saurayi.

Wanda ake tuhumar ya amsa laifin farko, yayin da ya musanta na biyun da ake tuhumarsa da shi, inda daga nan ne alƙakin ya ɗage zaman kotun zuwa 7 ga watan Satumba.

Alƙalin kotun, mai shari'a Nura Yusuf-Ahmad, ya ba da umarnin a ajiye Suleiman Shuaibu a gidan gyaran hali har zuwa ranar da za a dawo sauraron ƙarar kamar yadda Daily Nigerian ta wallafa.

Yan sanda sun kama ƙarin mutane 3 da suka yi wa sarkin Kano ihu

A baya Legit.ng ta kawo rahoto kan kamen da rundunar 'yan sandan jihar Kano ta ƙara yi na wasu matasa guda uku da ta zarga da shiga cikin waɗanda suka yi wa sarkin Kano Aminu Ado ihu.

Kara karanta wannan

"Ba Zan Yi Karya Domin Kare Gwamnatin Tinubu Ba" Sabon Minista Ya Yi Magana Mai Jan Hankali

Waɗanda aka kama matasa ne masu matsakaitan shekaru a ci gaba da binciken da rundunar ke gudanarwa.

A kwanakin baya ne dai aka samu wani gungu na matasa da suka yi wa sarkin na Kano ihu a yayin da ya zo bikin buɗe asibitin Hasiya Bayero da gwamnan Kano me ci ya gyara.

Hukumar tace finafinai ta kulle sutodiyon wani mawaƙi a Kano

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan kulle sutodiyon buga waƙoƙi na wani mawaki Idris Danzaki da hukumar tace finafinai da ɗab'i ta jihar Kano ta yi.

Hukumar ta ce ta garƙame sutodiyon mawaƙin tare da kwashe kayayyakin aikinsa bisa ƙin amsa gayyatar da ta yi ma sa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng