Abba Gida-Gida Ya Saki Miliyan 854 Don Auren Zawarawa a Jihar Kano, Zai Kuma Aiwatar Da Wasu Muhimman Ayyuka 2
- Gwamnatin jihar Kano ta sanar da sakin naira miliyan 854 don auren zuwarawa a jihar
- Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya bayar da sanarwar bayan taron majalisar zartawa na jihar a ranar Laraba, 23 ga watan Agusta
- Bayan nan majalisar ta amince da biyan yan fansho hakkinsu da kuma wasu gadojin sama guda uku
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Kano - Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da sakin Naira miliyan 854 domin daura auren zawarawa a jihar Kano.
Abba Gida-Gida ya ce sun yanke wannan hukunci ne yayin zaman majalisar zartarwa na jihar Kano wanda ya gudana a ranar Laraba, 23 ga watan Agusta.
Abba Gida-Gida ya amince da biyan yan fansho kudinsu
Hakazalika, a yayin taron majalisar, gwamnan na Kano ya kuma amince a biya gaba daya yan fansho da ke jihar kudadensu da suke bi.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Za a gyara gadojin sama uku a jihar Kano
Sannan gwamnatin Kano ta kuma amince da gyara wasu gadojin sama guda uku da dalibai ke bi wajen shiga makarantu a jihar.
Gadojin sune na bakin shiga tsohuwar jami'ar Bayero, gadar bakin kofar shiga kwalejin koyon ilimin addini ta Malam Aminu Kano da kuma gadar kofar shiga makarantar koyon ilimi mai zurfi ta Sa'adatu Rimi.
Ya rubuta a shafinsa na Twitter:
"Bugu da ƙari cikin zaman da majalisar zartarwa ta gudanar a jiya laraba karkashin jagorancina, majalisar zartarwa ta amince da abubuwa kamar haka:
"1- Mun saki kuɗi kimanin miliyan ɗari 8 da 54 (854m) domin fara gudanar da bikin auren zawarawa a jihar Kano.
"2- Na naɗa kwamiti na musamman da duba yadda zamu biya dukkanin ƴan fansho dake jihar Kano haƙƙoƙin su.
"3- Za'a gyara gadojin sama guda uku waƴanda suke taimakawa ɗalibai wajen shiga makarantun su a bakin ƙofar shiga tsohuwar jami'ar Bayero dake nan Kano, da kuma wacce take a bakin ƙofar shiga Kwalejin koyon ilimi addini ta Malam Aminu Kano hadi da gadar da ke ƙofar shiga makarantar koyon ilimi mai zurfi ta Sa'adatu Rimi. -AKY."
Abba Gida-Gida ya ware kudi don biya wa daliban BUK kudin makaranta
A wani labarin kuma, mun ji cewa gwamnatin jihar Kano ta amince da sakin kudi naira miliyan 700 domin biya wa dalibai 7,000 yan asalin jihar da ke karatu a jami'ar Bayero, BUK kudin makaranta.
Gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida shine ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na Twitter a ranar Laraba, 23 ga watan Agusta.
Asali: Legit.ng