Wike Zai Rushe Gidaje 6,000 a Unguwanni 30 a Abuja? Ministan Abuja Ya Yi Karin Haske

Wike Zai Rushe Gidaje 6,000 a Unguwanni 30 a Abuja? Ministan Abuja Ya Yi Karin Haske

  • Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya yi watsi da rahotannin cewa yana shirin rusa gidaje 6,000 da basa bisa ka'ida a fadin unguwanni 30 a Abuja
  • Tsohon gwamnan na jihar Ribas kuma jigon jam'iyyar PDP ya bayyana ikirarin a matsayin makirci tsantsa
  • Wike ya yi karin hasken ne a ranar Alhamis, 24 ga watan Agusta, a wata sanarwa da daraktan labarai na ofishin ministan, Anthony Ogunleye ya fitar

Abuja - Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya yi watsi da rahotannin da ke cewa zai fara aikin rusa gidaje 6000 a fadin unguwanni 30 a Abuja da kuma Wadata Plaza.

Wike ya bayyana hakan ne a wani rubutu da ya yi a shafinsa na Facebook a ranar Alhamis, 24 ga watan Agusta.

Kara karanta wannan

Wike Ya Bai Wa Yan Kwangila Wata 8 Su Kammala Aikin Layin Dogo Na Zamani a Abuja

Wike ya karyata rahotannin rusa gidaje 600 a Abuja
Wike Zai Rushe Gidaje 6,000 a Unguwanni 30 a Abuja? Ministan Abuja Ya Yi Karin Haske Hoto: Nyesom Ezenwo Wike/Abuja City
Asali: Facebook

Ministan ya bayyana wadannan rahotanni a matsayin karya kuma cewa babu kamshin gaskiya a cikinsu.

Wani bangare na sanarwar na cewa:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Ya zama dole mu yi magana kan labarai na baya-bayan nan a kafafen yada labarai, wadanda ke ikirarin cewa sabon Ministan Abuja, Barista Ezenwo Nyesom Wike, zai fara aikin rusa gidaje 6000 a cikin unguwanni 30 a Abuja da kumaWadata Plaza.
"Muna so mu bayyana cewa wadannan labaran gaba daya karya ne kuma bai da wani tushe a zahiri.
"Labarin rushe gidaje 6000 da wata jaridar kasar ta wallafa a ranar 22 ga watan Agustan 2023 da taken "Filin Abuja: FG na iya kwace filaye tare da rushe gidaje 6000 a unguwar talakawa" yayin da wata jaridar ta kuma wallafa wannan labarin mai tayar da hankali. "Za a ruguza Wadata Plaza, martani ya biyo bayan barazanar da Wike ya yi na rusau."

Kara karanta wannan

Makuden Miliyoyi: Farashin Motar Alfarma Ta Wike Mai Lamba 'FCT-01' Ya Bayyana, Yan Najeriya Sunyi Martani

Wike ya karyata fadin zai gyara Abuja cikin kwana 6

Ya kara da cewa, bai lissafo wasu wurare ko jerin gidajen da basa bisa ka'ida da za a cire ba a FCT, maimakon haka, ya nanata bukatar cire gidajen da basa bisa ka'ida ne a Abuja.

Wike ya kuma nuna rashin jin dadinsa kan wani rahoton da ke cewa zai gyara Abuja cikin kwanaki shida.

Ya ce:

"Muna son fayyace cewa babu wani lokaci da mai girma minista ya fadi haka ko ya yi ishara da wannan magana ta kowace hanya. Don haka, wannan kannen labaran an kirkire shi ne saboda makirki."

Wike ya ba yan kwangila wata 8 su gama aikin layin dogo na Abuja

A wani labarin, mun ji cewa a ranar Laraba, 23 ga watan Agusta, ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike ya bayar da sabon umurni game da aikin layin dogo.

Wike wanda ya nuna bacin rai a kan halin da layin dogon na Abuja ke ciki, ya umurci sakataren dindindin da ya biya kamfanin China da ke aikin cikakken kudi domin a kammala aikin gyaran hanyar jirgin kasan cikin wata takwas.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng