Umahi: Gwamnatin Tinubu Zata Gina Gada a Babban Titin Abuja Zuwa Lokoja
- Tsohon gwamnan Ebonyi kuma ministan ayyuka, David Umahi, ya ce FG zata gina gadar sama a titin Abuja-Lokoja
- Ministan ya ce za a gina gadar ne domin kawo karshen wahalhalun da ambaliya ke haifarwa a kan titin mai matuƙar muhimmanci
- Umahi tare da gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello sun ziyarci titin ne domin duba aikin gina hanyar da ke gudana yanzu haka
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Abuja - Ministan ayyuka, David Umahi, ya bayyana cewa ma'aikatarsa zata gina babbar gada a babban Titin da ya taso daga Abuja zuwa Lokoja, babban birnin jihar Kogi.
Mista Umahi ya ce gwamnatin Bola Tinubu zata gina wannan gada ne a matsayin hanya ɗaya ta warware yawan ambaliyar ruwan da ke yawan aukuwa a kan titin.
Rahoton Daily Trust ya ce ministan ya faɗi haka ne ranar Talata lokacin da ya kai ziyarar gani da ido domin duba aikin gina titin Abuja-Lokoja da ake ci gaba da yi.
Umahi tare da gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi da wasu daraktocin ma'aikatar ayyuka sun ziyarci wasu wuraren da ake aikin gina titin.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Meyasa FG zata gina gada a titin?
A cewar David Umahi, babban titin Abuja-Lokoja shi ne hanya ɗaya da ta haɗa shiyyoyin Kudu maso Gabas, Kudu maso Kudu da Kudu maso Yamma da birnin tarayya Abuja da Arewacin Najeriya.
Ya ce a saboda haka ya kamata a ba ta fifiko saboda muhimmiyar rawar da take takawa a rayuwar al’umma da tattalin arzikin kasa.
Vanguard ta ruwaito Ministan na cewa:
"Mun gani cewa yankin da ke fama da ambaliya a ko da yaushe shi ne Koton Karfe kuma mafita ɗaya tilo da muka gano ita ce gina babbar gada, ta yadda matafiya zasu bi su tsallake wurin."
"Hakan zai yi aiki saboda wurin na da tsawon kilomita 1.6, wanda zai ɗauki gadoji guda 5, sai mu nunka biyu."
"Don haka zamu tsara komai mu miƙa wa shugaban ƙasa don jin ta bakinsa domin burinmu mu warware matsalar har abada."
Ministan, ya bukaci ’yan kwangilar da ke gudanar da aikin hanyar da su yi amfani da kankare, inda ya kara da cewa za a sake nazari tare da sake fasalin kwangilar hanyoyin.
Malami Ya Bayyana Hukuncin da Kotu Zata Yanke Kan Zaben 2023
A wani rahoton kuma Malamin coci, Fasto Tony Anthony, daga Bode a jihar Abiya ya bayyana wahayin da aka masa kan karar da ke gaban Kotun zaɓe.
Faston ya bayyana cewa kotun PEPC zata ƙara tabbatar da nasarar shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu a zaben ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023.
Asali: Legit.ng