An Shiga Jimamin Rasuwar Babban Farfesa a Jami'ar UNILAG

An Shiga Jimamin Rasuwar Babban Farfesa a Jami'ar UNILAG

  • Jami'ar UNILAG ta shiga cikin jimami da juyayin rashin Farfesa Oladele Orimoogunje wanda ya riga mu gidan gaskiya
  • A wata sanarwa da shugaban jami'ar, Folasade Ogunsola, ta fitar ta ce Orimoogunje ya rasu ne a safiyar ranar Talata
  • Orimoogunje, kafin mutuwarsa Farfesa ne a sashen karatun ilmin harsunan Afirka da Asia (LAAS), na tsangayar 'Arts' kuma darektan 'Institute of Continuing Education' (ICE)

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Akoka, jihar Legas - Farfesa Oladele Orimoogunje, babban mamba a majalisar gudanarwa ta jami'ar jihar Legas (UNILAG), ya riga mu gidan gaskiya.

Orimoogunje, darektan 'Institute of Continuing Education' (ICE), ya koma ga mahaliccinsa ne a safiyar ranar Talata, 22 ga watan Agustan 2023.

Farfesa Orimoogunje ya bar duniya
Farfesa Orimoogunje ya koma ga mahaliccinsa Hoto: UNILAG
Asali: Twitter

A cewar wata sanarwa da aka sanya a shafin yanar gizo na jami'ar, babban farfesan ya rasu ne a asibitin koyarwa na jami'ar jihar Legas (LUTH), amma ba a bayyana abin da ya haddasa mutuwarsa ba.

Kara karanta wannan

"Akwai Babbar Matsala" Fitaccen Malami Ya Bayyana Hukuncin da Kotu Zata Yanke Kan Nasarar Tinubu a 2023

Rasuwar Orimoogunje ta girgiza mutane sosai inda aka shiga cikin jimami da takaici a jami'arta UNILAG.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugabar UNILAG ta sanar da rasuwar Oladele Orimoogunje

Shugabar jami'ar UNILAG, Farfesa Folasade Ogunsola, wacce ta rattaɓa hannu kan sanarwar, ta aike da saƙon ta'aziyyarta ga iyalan mamacin, inda ta bayyana rasuwarsa a matsayin babban rashi ga jami'ar.

A yayin da take aikewa da saƙon ta'aziyyarta a madadin jami'ar, shugabar jami'ar ta yi addu'ar Allah ya jiƙan marigayin.

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

"Jami'ar jihar Legas (UNILAG) na sanar da rasuwar Farfesa Ọládélé Caleb Orímóògùnjẹ́ na sashen karatun ilmin harsunan Afirika da Asia (LAAS), a tsangayar 'Arts'.”

Rasuwar Farfesa Oladele dai babban rashi ne ga jami'ar ta UNILAG duba da jajircewarsa wajen kawo cigaba jami'ar.

Farfesa Folagabade Ya Rasu

A wani labarin kuma, an yi babban rashi na ɗaya daga cikin shugabannin cocin Redeemed Christian Church of God (RCCG), wanda ya riga mu gidan gaskiya.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP Ta Fusata, Ta Dakatar da Shugaban Matasan Jam'iyyar a Jihar Arewa Kan Abu 1

Farfesa Folagabade Aboaba wanda shi ne mataimakin shugaban cocin, ya yi.bankwana da duniya ne bayan ya yi fama da ƴar gajeruwar rashin lafiya.

Fasto Folagabade Aboaba wanda na kusa da shugaban cocin ne Fasto Enoch Adeboye, ya mutu ne yana da shekara 90 a duniya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng