Yan Bindiga Sun Halaka Mutum 8 Kan Rikicin Shugabanci a Jihar Benue

Yan Bindiga Sun Halaka Mutum 8 Kan Rikicin Shugabanci a Jihar Benue

  • Rikicin shugabanci ya ɓarke a tsakanin ƴan bindiga masu ɗauke da makamai da.suka addabi mutane a jihar Benue
  • Ƴan bindigan sun kaure da faɗan ne a ƙoƙarin karɓe ikon wasu ƙauyuka guda biyu a ƙaramar hukumar Ukum
  • Rikicin na ƴan bindiga ya janyo sun halaka mutum takwas a tsakaninsu tare da ƙona kasuwar yankin

Jihar Benue - Ƴan bindiga sun halaka mutum takwas a rikicin shugabanci a ƙauyukan Chitto da Gbeji a ƙaramar hukumar Ukum ta jihar Benue.

Kashe-kashen na zuwa ne ƙasa da sa'o'i 48 bayan an halaka kwamandan rundunar tsaron dabbobi na gundumar Mbatian, Jarule Likita, a ƙaramar hukumar.

Yan bindiga sun barke da fada a Benue
Yan Bindigan sun halaka mutum 8 a rikicin Hoto: Theguardian.com
Asali: UGC

Ƴan bindigan na rikicin shugabanci ne

Jaridar Vanguard ta tattaro daga wata majiya a yankin cewa ƴan bindigan sun farmaki junansu ne domin karɓe ikon ƙauyukan, sannan suka ƙona kasuwar da ke yankin.

Kara karanta wannan

Akwai Matsala: Babban Malamin Addini Ya Fadi Wani Mummunan Abu Da Zai Faru a Najeriya a Mulkin Tinubu, Ya Fadi Mafita

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Majiyar wanda ya bayyana cewa har yanzu ana gwabza faɗan, ya yi bayanin cewa an halaka mutum biyar a ƙauyen Chitto ranar Litinin, yayin da aka halaka wasu mutum uku a ƙauyen Gbeji ranar Talata da safe.

"Ƴan bindiga sun halaka mutum biyar a ƙauyen Chitto na ƙaramar hukumar Ukum. Sun kuma ƙona kasuwar yankin." A cewarsa.

Haka kuma, wani majiya daga yankin ya bayyana cewa ƴan bindigan sun halaka mutum uku a kan hanyar Sankera-Chitto a ranar Talata, rahoton Daily Post ya tabbatar.

A kalamansa:

"Abin da na sani shi ne, ƴan bindigan faɗa su ke yi da junansu. Ina tunanin abin da ke faruwa kenan. Ɓangarorin biyu na faɗa da juna. Akwai sojoji a Zaki-Biam amma suna cigaba da cin karensu babu babbaka. Abun akwai takaici."

Abin da hukumomi suka ce kan lamarin

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Kai Sabon Farmaki a Arewacin Najeriya, Sun Halaka Bayin Allah Masu Yawa

Ɗan majalisar da ke wakiltar Ukum a majalisar dokokin jihar Benue, Ezra Nyiyongo, ya tabbatar da aukuwar lamarin inda ya bayyana cewa DPO na Ukum ya gaya masa cewa an ɗauko gawarwakin mutum uku daga wajen harin.

Lokacin da aka tuntuɓi kakakin rundunar ƴan sandan jihar, Catherine Anene, kan lamarin, ta bayyana cewa har yanzu ba ta samu rahoto ba a kai.

Yan Bindiga Sun Kai Hari a Katsina

A wani labarin kuma, ƴan bindiga sun kai farmaki a wasu ƙauyuka na ƙaramar hukumar Danmusa a jihar Ƙatsina.

Ƴan bindigan sun halaka mutum biyar tare da sace mata da dabbobi masu yawa a yayin harin da suka kai a ƙauyukan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng