Kafar Hagu: Ministar Tinubu Ta Fara Saba Doka, Ta Bayyana Manufofinta a Ofis
- Hannatu Musa Musawa ta fadawa mawaka su shirya fito da wakar da za ta zama taken Najeriya
- Sabuwar ministar ta na so a daina yi wa ‘Yan Najeriya kallon mutanen banza a kasashen waje
- Musawa ta watsa kudi wajen bikin taya ta murna, hakan ya jawo bankin CBN zai zauna da ministan
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Abuja - Hannatu Musa Musawa ta shiga ofis a matsayin minista fasaha da al’adu da tattalin arzikin kirkire-kirkire bayan rantsar da ministoci da aka yi.
A farkon makon nan labari ya fito daga The Cable inda aka ji Hannatu Musa Musawa ta na bayanin shirinta na fito da waka da za ta zama taken Najeriya.
Yayin da ta ke zantawa da manyan sakatarori, darektoci da sauran jami’an da ke ma’aikatarta, lauyar ta ce masu waka a kasar nan su fara shirye-shirye.
Akwai kudi a ma'akatar nan
A ranar Talata, Hannatu Musawa ta ce ta na so mawakan da ke duka bangarorin Najeriya su soma tunanin wakar da za a kirkiro a matsayin taken kasar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Musawa da aka tantance a majalisar dattawa ta ke cewa za a samu kudin shiga na kasar waje daga bangaren al’adun bayan ta kafa tarihi a matsayin mace.
Baya ga haka, rahoton ya ce ministar wanda ta saba rera wake, ta ce a shiryawa ganin sauyi ta yadda za a canza kallon da ake yi wa Najeriya a ketare.
'Yan Najeriya ba mutanen banza ba ne
Burin Musawa daga yanzu shi ne a daina ganin mutanen Najeriya da damfara da ta’addanci.
Kafin a fito da kowane irin tsari, sabuwar ministar tarayyar ta yi alkawari sai ta zauna da masu ruwa da tsaki domin a tattauna kafin a dauki mataki.
An lika takardun kudi
‘Yanuwa da abokan arziki sun shiryawa Barista Musawa liyafa domin taya ta murnar samun wannan mukami, a nan ne ake zargin tayi likin kudi.
Lika kudi da ake kira manni a wajen biki, ya sabawa dokar Najeriya. BBC ta ce a dalilin haka aka ji babban bankin kasar ya na barazanar kama ministar.
Shugaban sashen sadarwa na bankin, Isa Abdulmumin ya fadawa tashar cewa har yanzu dokar da aka sani ta na aiki, kuma za su tuntubi ministar tarayyar.
Samuel Ortom ya yabi Ministoci
Tsohon Gwamnan Benuwai, Samuel Ortom bai tallata Atiku Abubakar Bola Ahmed Tinubu, ana tunanin ya yi wa Peter Obi aiki ne a zaben da aka yi a 2023.
Amma da aka zo maganar shugabanci, ‘dan siyasar ya jinginar da adawa ya na yabon Nyesom Wike da Joseph Utsev da su ka zama ministoci a Najeriya.
Asali: Legit.ng