Abdulsalami Abubakar Ya Bayyana Yadda Tattaunawarsu Ta Kaya Da Sojojin Juyin Mulkin Nijar
- Janar Abdulsalami Abubakar ya yi bayani ga Shugaba Tinubu kan yadda zamansu ya kaya da sojojin juyin mulkin Nijar
- Tsohon shugaban mulkin sojan na Najeriya, ya bayyana cewa babu wanda yake son yaƙi sannan ya yi fatan cewaa za a warware rikicin cikin ruwan sanyi
- Abdulsalami ya bayyana cewa sojojin juyin mulkin sun gabatar da bayanansu a yayin zaman, waɗanda ya gayawa shugaban ECOWAS
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Fadar shugaban kasa, Abuja- Tsohon shugaban mulkin soja a Najeriya, Janar Abdulsalami Abubakar, ya fitar da sabon bayani dangane da halin da a ke ciki a Nijar, bayan ya kai ziyarar tattauna da sojojin da suka yi juyin mulki.
Abdulsalami, wanda ya jagoranci tawagar wakilan ECOWAS zuwa Nijar a ranar Asabar, 19 ga watan Agusta, ya bayyana cewa sun yi tattaunawa mai kyau da sojojin, domin ganin an dawo da ƙasar kan turbar dimokuraɗiyya, cewar rahoton The Cable.
Ya bayyana hakan ne bayan ya sanya labule da shugaban ƙasa Bola Tinubu, shugaban ƙungigar raya tattalin arziƙin ƙasashen Afirika ta Yamma (ECOWAS) a ranar Talata, 22 ga watan Agusta.
"Dole ne na bayyana cewa ziyarar mu zuwa Nijar ta biya kuɗin sabulu, kuma ta buɗe hanyar da za a fara tattaunawa sannan muna fatan za a cimma matsaya." A cewarsa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abdulsalami ya bayyana cewa sojojin juyin mulkin sun yi bayanansu, waɗanda ya gayawa shugaban na ECOWAS.
Juyin mulkin: Babu wanda yake son yaƙi
Ya bayyana cewa babu wanda yake son yaƙi sannan ya yi fatan cewa ba za a samu tangarɗa ba wajen warware rikicin ta hanyar diflomasiyya, rahoton The Punch ya tabbatar.
A kalamansa:
"Muna fatan za a warware rikicin cikin diflomasiyya. Babu wanda yake son yaƙi, amma shugabannin mu sun ce za a yi hakan idan har ba a samu mafita ba, wacce ba na tunanin ba za a sameta ba domin warware wannan taƙaddamar."
An Dakatar Da Nijar Daga AU
A wani labarin kuma, ƙungiyar tarayyar Afirika ta dakatar da Jamhuriyar Nijar daga matsayin zama ɗaya daga cikin mambobinta.
Ƙungiyar AU ta bayyana cewa za ta ɗage ƙasar ne kawai daga dakatarwar idan mulki ya tashi daga hannun sojoji.
Asali: Legit.ng