'Tinubu Na Yaudarar 'Yan Najeriya Da Kudin Tallafi Don Tilasta Karin Kudin Mai', COSEY

'Tinubu Na Yaudarar 'Yan Najeriya Da Kudin Tallafi Don Tilasta Karin Kudin Mai', COSEY

  • Kungiyar COSEY ta bukaci Shugaba Tinubu da ya dawo da tallafin mai don rage wa jama'a radadin da suke ciki
  • Shugaban kungiyar, Goodluck Ibem shi ya bayyana haka inda ya ce Tinubu ba shi da tausayi ko kadan
  • Ya ce Shugaba Tinubu na yaudarar 'yan Najeriya da kudaden tallafi don tilasta musu amincewa da karin kudin mai

FCT, Abuja - Gamayyar Shugabannin Matasan Kudu maso Gabashin Najeriya (COSEY) ta zargi Shugaba Tinubu kan yaudarar 'yan Najeriya da kudin tallafi.

COSEY ta ce Tinubu na amfani da Naira biliyan biyar da ya ware na tallafi don tilasta 'yan kasar amincewa da karin kudin mai a dole.

Tinubu na yaudarar 'yan Najeriya da kudin tallafi
Kungiya Ta Soki Tsarin Tinubu Na Karin Kudin Litar Mai. Hoto: Bola Ahmed Tinubu.
Asali: Facebook

Meye kungiyar ta ce kan Tinubu?

Kungiyar ta bukaci Tinubu ya mayar da kudin litar mai Naira 165 inda su ka ce shugaban ya mayar da 'yan kasar tamkar "fursunonin yaki", cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

Wani Dan Arewa Ya Sha Alwashin Canja Sunan Diyarsa Zuwa Sunan Mahaifiyar Tinubu, Ya Fadi Sharadi

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Shugaban kungiyar, Goodluck Ibem ya caccaki Tinubu da damfarar 'yan Najeriya wurin amfani da kudin tallafin don tilasta musu amincewa da karin kudin mai.

Wannan na zuwa ne bayan Shugaba Tinubu ya bai wa ko wace jiha Naira biliyan biyar da kuma tileran kayan abinci ga jihohi don rage radadin cire tallafi.

Ibem ya bukaci Tinubu da ya bar daukar 'yan Najeriya marasa wayo inda ya ce ya yi amfani da matsayinsa don inganta rayuwarsu ba wai kawo wahalhalu ba.

Meye kungiyar ta bukata gun Tinubu?

Ya ce:

"Yan Najeriya sun bayyana a fili su na bukatar a dawo da tallafin mai amma ya na yaudarar su da tallafin kudade da 'yan tsiraru ne za su samu.
"Wannan karin kudin litar mai ya tabbatar cewa Tinubu bai damu da wahalhalun da 'yan kasar ke ciki ba."

Kara karanta wannan

Juyin Mulkin Nijar: Da Gaske Janar Tchiani Ya Kira Gwamnatin Tinubu Da haramtacciya? Gaskiya Ta Yi Halinta

Kungiyar ta kara da cewa tun farkon hawan Tinubu ya kara kudin mai daga Naira 165 zuwa Naira 530, Newstral ta tattaro.

Tinubu ya kuma kara daga Naira 530 zuwa Naira 630 inda ta ce fiye da mutane miliyan 10 sun mutu saboda wahala.

Tinubu Zai Raba Naira Biliyan 5 Ga Ko Wace Jiha

A wani labarin, Shugaba Bola Tinubu ya ware makudan kudade don rabawa jihohi 36 Naira biliyan biyar ko wace jihar don rage radadin cire tallafi.

Gwamnan jihar Borno, Babagana Zullum shi ya bayyana haka ga manema labarai a ranar 17 ga watan Agusta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.