Uba Sani: Kaduna Zata Dauka Matasa 7,000 Aiki Domin Yaƙi da Matsalar Tsaro

Uba Sani: Kaduna Zata Dauka Matasa 7,000 Aiki Domin Yaƙi da Matsalar Tsaro

  • Gwamnatin Kaduna ta kammala shirin ɗaukar matasa 7,000 aikin ƙungiyar 'yan Bijilanti domin kawo karshen matsalar tsaro
  • Gwamna Malam Uba Sani ya ce zasu yi haka ne domin taimaka wa hukumomin tsaro a ƙoƙarinsu na dawo da zaman lafiya
  • Kaduna na fama da ƙalubalen tsaro kama daga ayyukan yan bindiga, garkuwa da mutane da sauran manyan laifukan ta'addanci

Kaduna state - Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna ya ce gwamnatinaa ta gama shirin ɗaukar matasa 7,000 aiki domin su taimaka wa hukumomin tsaro a ƙoƙarin magance matsalar tsaron jihar.

Jihar Kaduna da ke shiyyar Arewa maso Yammacin Najeriya, tana fama da ayyukan yan bindigan daji, masu garkuwa da mutane da wasu manyan ƙalubalen tsaro.

Gwamnan Kaduna, Malam Uba Sani.
Uba Sani: Kaduna Zata Dauka Matasa 7,000 Aiki Domin Yaƙi da Matsalar Tsaro Hoto: @ubasanius
Asali: Twitter

Amma a wani yunƙuri na kawo ƙarshen waɗannan matsaloli, gwamna Sani ya ce gwamnatinsa zata jawo matasa domin magance ayyukan ta'addanci a Kaduna.

Kara karanta wannan

Aljeriya Na Ba Nijar Wutar Lantarki Kyauta Bayan Najeriya Ta Dai Na Ba Su? Gaskiya Ta Bayyana

A cikin shirin Siyasa a Yau na kafar talabijin ɗin Channels ranar Litinin, Malam Uba Sani ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"A Kaduna, na farfaɗo da ayyukan 'yan bijilanti, kuma a yanzu da nake tattauna wa da ku, mako mai zuwa zamu ɗauki matasa 7,000 aikin 'yan bijilanti wato Kaduna State Vigilance Service.”

Dalilin ɗaukar matasa 7,000 aiki - Sani

Gwamnan ya ƙara da cewa wannan matakin ya zama tilas duba da yadda hukumomin tsaro suka rasa masu yi musu jagora a ƙoƙarinsu na dawo da zaman lafiya.

A rahoton jaridar Punch, Uba Sani ya ci gaba da cewa:

"Kuma ina da tabbacin cewa suna buƙatar taimakon yan Bijilanti, a yanzu muna da jami'ai 2,000 amma zamu ƙara ɗaukar mutane 7,000 domin su zama 9,000."
"Haka nan na ji daɗi saboda kwamishinan yan sanda, daraktan DSS da kwamandan sojoji da ke nan Kaduna, duk sun yi na'am zasu bada gudummuwa wajen horar da matasan."

Kara karanta wannan

Ministocin Tsaro: Badaru da Matawalle Sun Ɗauki Alkawari, Sun Faɗi Lokacin da Za'a Ga Sauyi a Tsaron Ƙasa

"Muna amfani da kwalejin horrar da jami'an 'yan sanda wajen horar da matasa 'yan bijilanti, wanda hakan yana da matuƙar amfani da tasiri."

Wasu matakai da Kaduna ke ɗauka

Baya ga haka, ya ce gwamnatin jihar na hada hannu da sauran masu ruwa da tsaki ciki har da kungiyoyin addini domin ganin an kawar da miyagun laifuka a Kaduna.

Uba Sani ya kuma ce akwai tattaunawar da suke da gwamnonin arewa don daidaita hanyoyin da za a magance rashin tsaro.

Sanatan Ogun Ta Tona Asirin Waɗanda Suka Hallaka Babban Hadiminsa

A wani rahoton kuma Sanata mai wakiltar Ogun ta yamma a inuwar APC, Solomon Adeola, ya bayyana waɗanda suka kashe hadiminsa a Legas

A wata sanarwa da ya rattaɓa wa hannu da kansa, Sanatan ya ce wasu sojoji ne suka bindige marigayi babban hadiminsa har lahira.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262