"Na Rubuta Wasika Zuwa Ga Shugabannin PDP Kafin Na Karbi Mukamin Minista", Wike
- Tsohon gwamnan Rivers kuma ministan Abuja, Nyesom Wike ya gargadi masu yada jita-jita a kansa da su guji hakan ba tare da sun san komai ba
- Wike na magana ne kan cece-kucen da ake yi a kansa bayan nada shi mukamin minista da Shugaba Bola Tinubu ya yi a gwamnatinsa na APC
- Ya ce sai da ya rubuta wasika ga shugaban jam’iyyar PDP da sauran masu ruwa da tsaki inda ya ce sun amince masa ya karbi mukamin
FCT, Abuja – Ministan Abuja, Nyesom Wike ya bayyana cewa nada shi minista ya samu goyon bayan jam’iyyarsa ta PDP.
Ana zargin Wike wanda ya kasance tsohon gwamnan jihar Rivers kuma tsohon minista a gwamnatin PDP da yi wa APC aiki a zaben da ya gabata, Legit.ng ta tattaro.
Meye Wike ya ce kan mukamin minista?
Wike ya bayyana haka ne yayin da ya ke magana da ‘yan jaridu a yau Litinin 21 ga watan Agusta jim kadan bayan an rantsar da shi.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ya ce ya rubuta wasika zuwa ga shugaban jam’iyyar PDP da kuma sauran masu ruwa da tsaki a jam’iyyar kan mukaminsa, ya ce kuma dukkansu sun yi martani kan wasikar.
Wike ya ce har gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara ya ba shi daman karbar mukamin.
Ya ce mutane su bar yada jita-jita da farfaganda a kan abin da ba su da masaniya a kansa.
Meye martanin PDP kan wasikar Wike?
Ya ce:
“Na rubuta wasika zuwa ga shugaban jam’iyyar PDP, na rubuta zuwa ga shugaban marasa rinjaye a majalisar Dattawa da ta Wakilai.
“Na kuma rubuta zuwa ga shugaban jam’iyyar na yanki da kuma gwamnan jihar Rivers kuma dukkansu sun yarda da hakan.”
Yayin da ake daf da zaben watan Faburairu na wannan shekara, Wike da sauran gwamnoni guda hudu sun fita sha’anin dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar.
Bijirewar ba ta rasa nasaba da rikicin shugabancin jam’iyyar da kuma gazawa na tsohon shugaban kasar wurin hada kan ‘yan jam’iyyar, Daily Post ta tattaro.
Tinubu Ya Rantsar Da Sabbin Ministoci
A wani labarin, Shugaba Tinubu ya rantsar da sabbin ministoci a yau Litinin 21 ga wata Agusta.
Nyesom Wike na daga cikin wadanda su ka karbi rantsuwar kama aiki a matsayin minista.
Asali: Legit.ng