Sanatan Ogun Ta Tona Asirin Waɗanda Suka Hallaka Babban Hadiminsa
- Sanata mai wakiltar Ogun ta yamma a inuwar APC, Solomon Adeola, ya bayyana waɗanda suka kashe hadiminsa a Legas
- A wata sanarwa da ya rattaɓa wa hannu da kansa, Sanatan ya ce wasu sojoji ne suka bindige marigayi babban hadiminsa har lahira
- A ranar Asabar, 5 ga watan Agusta, aka harbe babban hadimin sanatan, Adeniyi Sanni, a hanyarsa ta komawa gida
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Ogun state - Sanatan Ogun ta yamma, Solomon Adeola, ya ce ya gano wadanda suka kashe babban hadiminsa, Adeniyi Sanni, wanda aka harbe har lahira a jihar Legas da safiyar ranar Asabar.
An harbe Mista Sanni ne a lokacin da yake kan hanyarsa ta komawa gida, sannan aka jefar da gawarsa a kusa da wani barikin sojoji da ke kusa da tashar motar Toyota a Oshodi.
Sanata Adeola, shugaban kwamitin kasafin kuɗi a majalisar dattawa, ya ce binciken da aka gudanar ya bayyana cewa wasu sojoji da ba a gane ko su waye ba ne suka bindige marigayin.
Ya ce jami'an hukumar sojin sun halaka marigayi Mista Sanni a daidai shingen binciken ababen hawa da ke yankin Ikeja a jihar Legas, kamar yadda Premium Times ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanatan ya yi wannan zargin ne a cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu da kansa a ranar Litinin kuma aka raba wa manema labarai.
Sanata Adeola ya fallasa yadda lamarin ya faru
Mista Adeola ya ce, binciken da aka yi kan lamarin mutuwar hadiminsa ya nuna cewa sojojin sun tare motar marigayin ne a wani shingen binciken sojoji da ke unguwar Ojodu-Berger a Legas.
Bayan tare shi ne jami'an sojin suka buƙaci ya nuna masu takardun shaidar mallakar motar da yake ciki kuma a wannan lokacin ba bu takardun motar a tattare da shi.
A cewarsa, bisa haka mamacin ya kira matarsa domin ta turo masa da Hotunan takardun motar ta shafin sada zumunta watau Whatsapp.
A rahoton The Cable, Mista Adeola ya ƙara da cewa:
"“An gano cewa matar ta sake kiran waya bayan wani lokaci, kuma marigayi Sanni ya shaida mata cewa sojoji na ci gaba da duba takardar motar. Wannan shi ne karo na karshe da ta ji ta bakin mijinta."
"Daga bisani kuma aka tsinci gawar Mista Sanni cike da harsasan bindiga a unguwar Toyota Bus Stop da ke Oshodi, kusa da wani barikin sojoji."
Sanatan ya yi kira ga babban hafsan sojin kasa, Taoreed Lagbaja, da ya bayar da umarnin gudanar da bincike cikin gaggawa kan kisan tare da gurfanar da duk wani jami’in da aka samu da hannu a aikata laifin.
Yan Bindiga Sun Harbe Kwamandan Rundunar Tsaro Har Lahira
A wani rahoton kuma Wasu mahara da ba a san ko su waye ba sun kashe kwamandan gunduma na rundunar kula da kiwon dabbobi a Benuwai.
Rahoto daga bakin waɗanda abun ya faru a idonsu ya nuna cewa kwamandan ya mutu ne bayan maharan sun harbe shi a ƙirji.
Asali: Legit.ng